Nice ƴar gidan Sayyid Ibrahim zakzaky, babban wanda akafi zalunta a duniya.
Nice ƴar gidan ummah zeenah, wacce tafiya ma bata iyayi a halin yanzu.
Nice ƙanwar yaya ahamad Wanda akai masa kisan gilla bayan azabtar wa.
Nice ƙanwar Sayyid hameed wanda aka caccakawa wuƙa a goshin sa har yayi shahada.
Nice ƙanwar Sayyid Mahmud, wanda aka harbe a tsakiyar titi batare da yayi komi ba.
An harbi ƙanina Sayyid Ali a gaban idona, kisa mai munin da ban iya misaltawa.
An harbi ƙanina humaid inna ji inna gani, babu damar dazan iya taimakawa.
An harbi ƙanina hammad, wanda harsa shi ya yanka wuyan sa, shima nan yafaɗi gaban idona.
A gaban idona ne aka dinga buɗe wuta cikin ɗakin da muke, da nufin a harbe mu, nida mahaifana.
A gaban idona aka harbi mamata zeenah a ƙoƙarin ta nabawa babana kariya, wanda akai mata harbi dayawa.
A gaban idona
sojoji suka zagaye babana kowa yana harbin sa, har takai da baya iya cewa komi!!!
A gaban idona wani soja ya mari babata, yakuma jamin hijabi da nufin yagawa.
A gaban idona aka ja mamata àƙasa ana dukan ta, batare da tai laifin komai ba.
A gaban idona sojoji suka ja babana suka ɗora shi a baro dan tsabar izgilan ci.
Sun harbe almajiran babana sama da mutum dubu maza da mata, da yara, da tsofaffi.
Sun harbi ƙawaye na wanda muka taso tun yarinta bamu rabuwa yau babu su.
Sun ƙone ƙanwar babana gwagwago fatima tanaji tana gani wuta wuta tanacin ta, har tayi shahada.
Sun ƙone abokan yayana Sayyid ahamad Wanda suka jima suna tare.
Taya ya zan samu nutsuwa arhali babata bata iya tafiya sai ta dugara sanda!!
Taya ya zan samu nutsuwa arhali babana kusan koda yaushe sai jinin sa ya hau!!
Taya ya hankali zai kwanta arhali an rushe gidan mu.
Taya ya hankali na zai kwanta arhali na rasa mataimaka!!!
Allah kaine gatan mu kuma kana gani, ka ƙwato mana Hakkinmu