Nayarda Malam Abduljabbar ya yi Manyan laifuka guda hudu

 - Daga Aliyu Dahiru


1. Ya yí fada da Salafíyya. 


2. Ya yí fada da yan haqíqa. 

3. Ya yi fada da wasú yan Qadiríyya

4. Ya yí fada da wasú yan síyasa. 


Wadannan sú súka hadu súka mayar da fadansu céwa na zagín Annabí (saw) né alhalin su kansu sun san karya suke. 


Nì daí da Annabi (saw) ya yí arahar da zan yì siyasa da shi, gwara a yau rayuwata ta fi. Anya wasu sun yarda idan an mutu za a tashi kuwa? 


Na yi imani bayan wannan rayuwar akwai wata rayuwar mafi muhimmanci da adalci. Ta yaya zan iya kallo Annabi (saw) a ranar alkiyama tare da na san na yi amfani da shi a duniya wajen bukatuna? 


Zan iya mutuwa a yanzu-yanzu ko an jima. Ko wani  bai kasheni ba, zan mutu a gida ko asibiti. Daga karshe dai duk mutuwa zamu yi ko mun shirya ko bamu shirya ba, kuma babban abin da zamu tarar shi ne abin da muka kudirta ko muka aikata. 


Fatana Ubangiji Ta'ala ya sa duk rintsi ya haneni siyasantar da addini ko karfafa masalahar duniyata fiye da ta lahirata. Ubangiji kada ka bari rashin tsoronka ya sa mu aikata zalinci da sunanka ko mu goyi bayan zaluncí da súnanka.

ماذا تقول؟ 

Mé za kúce ?

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post