1. Ya yi fada da Salafiyya.
2. Ya yi fada da yan haqiqa.
3. Ya yi fada da wasu yan Qadiriyya
4. Ya yi fada da wasu yan siyasa.
Wadannan su suka hadu suka mayar da fadansu cewa na zagin Annabi (saw) ne alhalin su kansu sun san karya suke.
Ni dai da Annabi (saw) ya yi arahar da zan yi siyasa da shi, gwara a yau rayuwata ta fi. Anya wasu sun yarda idan an mutu za a tashi kuwa?
Na yi imani bayan wannan rayuwar akwai wata rayuwar mafi muhimmanci da adalci. Ta yaya zan iya kallo Annabi (saw) a ranar alkiyama tare da na san na yi amfani da shi a duniya wajen bukatuna?
Zan iya mutuwa a yanzu-yanzu ko an jima. Ko wani bai kasheni ba, zan mutu a gida ko asibiti. Daga karshe dai duk mutuwa zamu yi ko mun shirya ko bamu shirya ba, kuma babban abin da zamu tarar shi ne abin da muka kudirta ko muka aikata.
Fatana Ubangiji Ta'ala ya sa duk rintsi ya haneni siyasantar da addini ko karfafa masalahar duniyata fiye da ta lahirata. Ubangiji kada ka bari rashin tsoronka ya sa mu aikata zalinci da sunanka ko mu goyi bayan zalinci da sunanka.
- Copied