(1) A cikin shekara ta alif dari tara da sittin da daya (1961) jami'ar Azhar ta bashi shaidar wa'azi da shari'a.
(2) A shekara ta alif dari tara da sittin da takwas (1968) Gidan sheikh Abdulkadir jilani na Bagdad sun nadashi shugaban darikar kadiriyya na Africa ta yamma ,
(3) A shekara ta alif dari tara da saba'in da hudu 1974 Sarkin Musulmai Abubakar na III (3) ya nada shi sarkin yakin sheikh Usmanu dan fodiyo.
(4) Bayan sheikh Nasir Kabara ya rubuta littafinnan me suna "KAM'UL FASADI FI TA'AYIDI SUNNATI SADALU" to ananne babban malamin nan mutafannini Sheikh Adamu Cindo yake bayyana matsayin sheikh Nasir kabara cewa shine fardi a wannan zamani.
(5) A karo na biyu gidan sheikh Abdulkadir jilani sun kara bashi matsayin shugaban darikar kadiriyya na Africa gabadaya a 1986.
(6) Kungiyar da'awa ta kasar Libya ta bashi matsayi (15).
(7) Jami'ar Saddam Husain ta Bagdad ta bashi matayin dattawan Jami'ar Saddam.
(8) A cikin shekera ta alif dari tara da da casa'in da shida 1996 Jami'ar Undurman ta kasar sudan ta bashi shaidar Digirin girmamawa
(9) Bayan rasuwar malam Nasir kabara a cikin shekara ta alif dari tara da casa'in da bakwai (1997) Jami'ar Ahmadu Bello Univercity Zaria itama ta bashi Digirin girmamawa.
Allah ya Kara kare malam da karewarsa