MUHIMMAN ABUBUWA 14 DA SUKA AUKU A WATANNIN "JULY" BAYAN WAKI'AR ZARIYA

 


Daga Saifullahi M. Kabir 


NA DAYA

9 Ga July, 2019;

A wannan ranar yan uwa sun gudanar da gagarumar Muzaharar kira a saki Shaikh Ibraheem Zakzaky a gaban Majalisar Tarayya a Abuja. 'Yan sanda sun dira a kan 'yan uwan inda suka Shahadantar da mutum biyu; Shahid Jafar Mika'il Lafia da Shahid Mahmud Umar Sakafa, tare da jikkata da dama. Sun kuma kama mutum 40 wadanda sai bayan lokaci mai tsawo kotu ta ba da belinsu.



 

   Wannan kazamin harin da ya auku, ya ta da hankalin yan Majalisar Wakilai sosai, inda a ranar 11/7/2019 suka yi kira kan gwamnatin tarayya ta yi dubi zuwa ga lamarin sakin Shaikh Zakzaky ko sa huta. Sai dai a wannan lokacin su kuma yan Majalisar Dattawa sun soki 'yan uwa ne a kan Muzaharar da suke yi. 


NA BIYU

11 Ga July, 2019;

A wannan ranar, an yi Waki'o'i a Abuja da Kaduna. Inda yan sanda suka dirarwa yan uwa masu Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky a daidai Sakatariyan Gwamnatin Tarayya a Abuja, suka jikkata da dama, suka kama kwarorin yan uwa. 

   A Kaduna kuwa, 'yan sandan sun bude wuta ne sosai kan masu Muzaharar, inda suka kashe yan uwa biyu; Shahid Ahmad Nasir Maraban Jos da Shahid Abubakar Aliyu Badikko. 


NA UKU

15 Ga July 2016:

A ranar 15 ga watan July, 2016 ne kwamitin binciken Kisan kiyashin Zariya da Elrufa'i ya kafa (JCI) ta mika rahoton bincikenta gare shi. A cikin rahoton Kwamitin ta nemi gwamnati ta hukunta GOC na rundunar soji ta daya da ke Kaduna, Major Janar Adeniyi Oyegbade, wanda ya furta da kansa a wani taron yan jarida da ya kira a ranar 14/12/2015 a Kaduna cewa shi ne wanda ya karkasa sojoji suka mamaye gurare uku; Husainiyya, Gyallesu da Darur Rahma akan duk yadda za a yi su kamo Shaikh Zakzaky. Don haka a kokarin wannan suka kashe mutane fiye da 1,000 kafin su kai ga Shaikh Zakzaky din. 


NA HUDU

16 Ga July, 2019;

A wannan ranar gamayyar 'yan sanda da 'yan iskan gari suka afkawa yan uwa masu Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky a Bypass, Kaduna, suka raunata mutum biyu, daya a kafa, daya harbi a kirji. Daga baya Allah Ya wa daya daga wadanda raunata din mai suna Shahid Nura Lawal (Markaz) cikawa. 


NA BIYAR

18 Ga July, 2019;

A wannan ranar aka sake shiga kotu a Kaduna don neman damar barin Shaikh Zakzaky da Malama Zeenah su tafi jinya a kasar waje, saboda halin da suke ciki ya kai wa ga ba su iya zuwa kotun ba ma a ranar. Amma lauyan gwamnati, Bayero Dari ya nemi kotun a karkashin Alkali Darius H. Koboh, ya basu mako guda don rubuta takardar martani ga lauyoyin Malam da suka kawo 'Medical Report' cewa bashi da lafiya. Nan Alkalin ya dage shari'ar zuwa 29/7/2019.


NA SHIDA

22 Ga July, 2019;

A wannan Ranar gamayyar Jami'an yan sanda da Mopol da DSS suka dira a kan yan uwa masu Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky a daidai Federal Sectariat, Abuja, inda suka yi harbin ba ji ba gani, suka kashe mutane fiye da 10. Sai dai mutane shida aka iya samun gawarwakinsu aka yi musu Janaza washe-gari aka bizne su a Darur Rahma, sune:

1- Shahid Hamisu Ibrahim Magaji, 

2- Shahid Husaini Yahya Soba, 

3- Shahid Ali Haidar Ibrahim, Rinji, 

4- Shahid Dahiru Tudun Wada Kaduna, 

5- Shahid Abubakar Isma'il Yola, 

6- Shahida Batula Muhammad Dakwa, Suleja 

   A wannan ranar 'yan sanda sun kashe Mataimakin Kwamishinan yan sanda tare da wani dan Jaridar gidan Channels TV da bindiga. 

   Sannan kuma sun kama 'yan uwa maza kimanin 55 da mata 6 har yau shekara guda kenan suna tsare da su a Kurkukun Kuje, Abuja da Kurkukun garin Suleja, bayan da suka shafe watanni kusan hudu a hedikwatar SARS a Abuja. 

  Jami'an tsaron sun je har asibiti a Gwagwalada suka sace marasa lafiya da gawargwaki suka tafi da su. Wannan yasa aka kai su kotu kara a kan kotun ta sa su ba da gawarwakin da suka sace. Kuma a wannan watan July din, shekara guda kenan da sace su din, kotu ta tabbatar da hakan da yan sanda suka yi ya sabawa ka'ida. Kuma ta yanke hukunci su maidawa yan uwa gawarwakin, sannan su biya diyyar naira miliyan 15 na gawarwakin da suka sace. 


NA BAKWAI

23 ga July, 2019;

A wannan ranar ma yan uwa sun sake fitowa Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky a kasuwar Wuse, Abuja, inda yan sanda suka sake bude wuta, sai dai ba su kashe kowa ba, amma sun kama yan uwa 14 rannan. Washe garin rannan 24/7/2019 suka kama wani dan uwa mai suna Mahdi suka rika masa azaba, suka kokkona jikinsa, sannan suka jefar da shi suka tafi. 


NA TAKWAS

25 Ga July, 2018:

A wannan ranar yan uwa sun hadu a Darur Rahma don addu'ar tunawa da Shahidan Quds na 2014 da Sojojin Jonathan suka kashe, wato taron tunawa da Shahidan karo na hudu. A daidai lokacin da ake gudanar da taron sai yan sanda suka zo suka kewaye wajen suka fara harbi, har suka raunata mutane hudu tare da kama wasu. Sai daga baya kotu ta ba da belinsu. 


NA TARA

26 Ga July, 2019;

A wannan rana ce Gwamnatin Buhari ta fitar da sanarwar ta ayyana Harkar Musulunci a matsayin kungiyar Ta'addanci, kuma ta haramta ta a fadin tarayyar Nijeriya. Gwamnatin wanda ta sanar da hakan a manyan jaridun kasa ranar 27/7/2019, ta ba da sanarwar hakan ne bayan samun dama daga wata Babbar kotun Tarayya da ke Abuja, a karkashin Alkaliya Nkeonye Maha. 

   A ranar 28/7/2019 Harkar Musulunci ta gabatar da taron manema labarai a Abuja, inda Farfesa Dahiru Yahya ya yi bayani ga yan jaridun a madadin Harka, ya jaddada cewa mu ba haramtattu bane a wajen Allah (T), kuma ba za mu taba zama haramtattu ba face a wajen shaidanu. Tare da bayyana Harkar Musulunci a matsayin mafita ga al'ummar Nijeriya ba barazana ba kamar yadda gwamnatin Buhari ke kokarin nunawa. 

   Bayan hakan, bangaren da ke lura da shari'a na Harkar Musulunci, sun kai gwamnatin tarayyar kotu, suna masu kalubalantar haramtawar da kotun ta ba da izinin ai wa Harka. Shari'ar da ke ta jan kafa har zuwa yanzu. 


NA GOMA

29 Ga July, 2019;

A wannan rana aka koma kotu a Kaduna don cigaba da shari'ar da gwamnatin Kaduna ke wa Shaikh Zakzaky, inda aka saurari batun yiwuwar barin su Malam Zakzaky da Malama Zeenah su je asibiti a India. Sai dai bayan sauraron nema da martanin, alkalin ya dage ranar yanke hukunci zuwa 5/8/2019. Kuma da ranar ta zo, ya ba da umurnin a bar su Malam su je asibitin India don yin jinyar jikinsu. Tafiyar da aka yi ba a samu nasarar jinya ba aka dawo bayan kokarin gwamnati na hargitsa shirin. 


NA SHA-DAYA

29 Ga July, 2019;

Wata jaririyar Kungiyar Shi'a mai suna Rasulul A'azam Foundation (RAAF) ta yi taron manema labarai a garin Gombe, inda suka bayyana cewa su ba suna tare da yan Harkar Musulunci a Nijeriya da gwamnati tace ta haramta su bane. Suka ce su yan Shia ne masu biyayya ga gwamnatin kafirci da goyon bayan tsarin kwansitushen da Baturen Ingila ya gadar mana bayan ya rushe tsarin Musulunci da Alkur'ani da Shehu Danfodiyo ya bari a kasar. 


NA SHA BIYU

30 Ga July, 2019;

A wannan ranar ne wani mutum mai suna Ustaz Hamza Lawal, wanda ke shugabantar wata kungiya da ya kafa bayan ya balle daga Harkar Musulunci, mai suna Assaqalain, ya kira taron manema labarai, inda ya kara jaddadawa gwamnati cewa shi ya jima da fita daga Harka Islamiyyah, shi ba dan gwagwarmayar kafuwar addini bane, shi dan Shi'a ne kawai mai goyon bayan tsarin Dumukuradiyya da Wila'a ga Kwansitushen din da Baturen Ingila ya dankara mana. Yayi wannan a kokarinsa na wayar da kan gwamnati kar garin kawowa masu gwagwarmayar addini hari ta hada da shi. 


NA SHA-UKU

31 Ga July, 2016;

A wannan rana ce wasu yan uwa suka yi hatsarin mota a kan hanyarsu ta dawowa Kaduna daga wajen taron tunawa da Shahidan Quds karo na biyu da aka gudanar a Abuja, kuma Allah (T) Ya kaddara rasuwar Malam Haruna Yusuf Shalleng (daya daga cikin Hadiman Shaikh Zakzaky), da Malam Mika'il Abdullahi (me shafin zane na "Hakeem Raji" a jaridar Almizan). A yayin da yan uwa biyu; Dr. Shuaibu Musa da Malam Haruna Abdullahi (Elbinawi) suka samu raunuka da karaya.


NA SHA-HUDU

31 Ga July, 2018;

A wannan ranar ne wata babbar kotun tarayya a jihar Kaduna (Federal High Court, Kaduna) ta sallama tare da wanke yan uwa 89 daga cikin wadanda sojoji suka kama bayan sun kashe fiye da mutum 1000 a Zariya. An kai yan uwan kotu ne bisa tuhumomi daban-daban daga ciki har da na kashe wani kurtun Soja a yayin da Sojojin suka kawo musu hari. Sai dai bayan 'yan uwan sun shafe kimanin watanni 31 ana tsare da su a Kurkukun Kaduna ana musu Shari'a, kotun ta wanke su daga dukkan zargin da ake musu ta sake su. Ragowar yan uwan ma daga baya wata kotun ta wanke su ta sallame su.


BAYANI:

Na ciro bayanan ne daga littafin MUHIMMAN RANEKU 400 A TARIHIN HARKAR MUSULUNCI da Cibiyar Wallafa  ta wallafa.



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post