__Sheikh Ibrahim Zakzaky (H)
"Me yasa Al'ummar Nigeria ba za su taru su koma hakikanin Addinin Allah ta'ala da aikata shari'ar da fiyayyen halitta Annabi muhammad (S) ya zo musu da shi ba.?
An dauki Lokaci ana cikin rudu, kullum ana tunanin ta ina ne za a samu mafita daga halin da ake ciki, amma kullum abin sai kara tabarbarewa yake yi.
An yi mulkin da ake cema, mulkin soja, an wuce, bai haifar ma kowa da 'Da mai ido ba. aka rankayo mulkinda ake kira "Democradiyya" ga shi nan shekara da shekaru ana cikinta, amma kullum cewa ake yi gumma jiya da yau.
P.D. PEEE! POWER!! Haka sukai ta kira a lokutan baya, sai PDP ta zama Power a kansu ba a gare su ba, ance ana mulkin 'Democracy' ne, amma kuma ga irin romon Democracy din da ake ta sha anan.
HIRAR JAGORA (H) DA ABS CHANNEL KAN WAKI'AR BUHARI.
..
18/12/2022