Matsalolin Da Lokuttan Fadarsu Ga Mai Gida.....!!!



@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@


Daga Littafin Zama da Miji, na Marigayiya Wasila Ahmad (Ummin Sajjad) 


Babu wani mutum da bashi da matsala alhalin yana cudanyuwa da wannan rayuwan na yau da kullum. Ko wane mutum yana son ya samu wanda zai rika tausaya masa, sannan kuma ya rika sauraron matsalolinsa, amman abin da ya kamata mu kula da shi shine akwai lokaci da kuma muhalli na yin komai.


Ya kamata ‘yar’uwa tasan cewa akwai lokuta na kaiwa maigida koken matsalolinki da kike fuskanta a gidanshi, wasu daga cikin mata ba su kan kula da irin wannan yanayin ba domin idanuwansu kan rufe da son kansu ba tare da duba shi wanda za ta kai wa koken ba, na yanayi da kuma halin da yake ciki.


Miji ya dawo gida ba kisan da wane yanayi ya shigo ba, ba kuma kisan ya yanayin aikinsa na wannan ranar yazo mashi ba, madadin a bashi awa daya zuwa biyu ya dawo hayyacinsa, a’a babu wannan, take yanke za’a fara jero mashi matsalolin gida wadda bai ma san ta ina zai fara ba.


 Misali za ka ji mace da shigowar miji gida za ta fara rattafo mashi matsala NTA farrrr.... “Ka tafi ka barni da yara basa jin magana ko kadan, Ahmad ya fashe glass din kofa, Khadija ta yi fada da yara a waje, Sadiq ko kadan baya maida hankali a makaranta, duk sun bi sun haukatani da rashin jinsu, dama dai ban haihu ba don babu ta inda suke taimako na, haka kuma babu mai sauraron kokena."


“Au! na ma manta kanwarka ta zo tana tamun babbotai kamar na ci gadon babanta, ko me ke damunta ban sani ba. Allah dai ya tsareni daga mahaifiyarka domin mugayen kalaman da takeyi a bayan idona suna cimun tuwo a kwarya, gashi haka kawai na je na datse hannu dazun da wuka...”


Ko kuma: “Da na sani da banje bikin gidan Muhammad ba, kai ka ga irin shigar da matar Abdurrashid ta yi? Hmmm! Allah ya sa dai nima inyi irin wannan dacen, wasu mazan suna kaunar matansu, ka ga suna siya masu kaya na kawa da kece raini, wadannan sune cikakkin maza. A lokacin da Abdurrashid ya fito sai da kowa ya girmamashi, gaskiya ne mutane na girmamaka da yanayin shigarka, shin me matarsa ta fi ni da har take jin kanta a gabana, ko da yake ta yi sa’ar miji mai sonta ba."


Kila ma ta kara da cewa: "Don haka ni ba zan iya zama cikin wannan gidan ba, wahalanka dana yaranka su kashe ni. Allah Ya kawo min canjin alkairi.”


Haba! Haba!! ‘Yar’uwa! Hakika wannan mummunar dabi’a ce. Mata masu irin wannan wawan tunanin tsammaninsu mazajensu na fita ne tun safe domin su je su shakata, ba su san irin gumurzu da wahalan da suke fuskanta ba kullum suka bar gidansu, kuma duk don ya maida ta irin waccan matar ta Abdurrashid da ta gani ta tsone mata ido.


Ki sani ya ke ‘yar’uwa, baki san irin abin da mai gidanki yake ratsowa ba idan ya fita wajen aikinsa, ba ki san kalan mutanen da yake cudanya da su ba, a lokacin da ya dawo gida kar ki rufeshi da matsalolinki a lokaci guda, kar ki sa ya zargi kansa akan kasancewarsa namiji ko mijinki. Ki zamto mai adalci ta hanyar kula da yanayinsa, idan kika cika shi da yawan koke za ki harzukashi don ba ki san abin da ya shigo da shi ba, kila ma matsalan da ke kansa ya fi naki amman bai hana shi kullum ya fita domin nema ba. To ki sani hakan da ki ka yi ba wayau bane, ba kuma dabara bace tunda ba zaki iya warware matsalanki ba ko daya ta wannan hanyar, karshe ma ki karawa kanki wani bacin ran.


A madadin hakan sai ki samu lokacin da ya dace ki fadawa mijinki dukkanin matsalolinki cikin hikima da dabara ba tare da nuna masa gajiyawarsa a kanki ba. Hakan zai sanya ya fahimce ki cikin sauki, kuma zai daukeki mai tausayinsa kuma abokiyar rayuwa ta gari kuma zai baki lokaci ku zauna domin tattauna matsalar gidanku ku kuma samu hanyar warwareta cikin sauki da izinin Allah (T).


A wani Hadisi Manzon Allah (S) yace: “Sallar macen da take aibata mijinta ba karbabbiya bace a wajen Allah, ko da tana azumi a ko wace rana sannan tana ayyukan ibada kowane dare, ko da ta ‘yanta bayi, ta bada dukiyarta ta hanyar Allah, amman tana munana kalamai a kan mijinta, ita ce farkon wadda za ta shiga wuta.”


Sannan a wani wajen Manzon Allah (S) yace: “Matayen Aljannah (Hurul-een) za su ce da wadannan matan masu wulakantar da mazajensu; ‘Allah ya kasheki kar ki cutar da mijinki, wannan ba mijinki bane, sannan baki cancanci zama matarshi ba, babu jimawa zai barki ya taho zuwa garemu.”


Ki dubi wadannan hadisan yar’uwa shin ba su baki tsoro ba? Ya ya zakie watsar da rayuwarki ta din-din-din akan wata rayuwa marar tabbas, wadda duk dadewanta ba za ki wuce shekara dari a cikinta ba? Yar’uwa ki yi wa kanki karatun ta natsu, ki sani kina rushe farin cikinki ne ki shiga kunci a nan duniya sannan kuma lahira ki karbi sakamakon aikinki a nan duniya kamar yadda ki ka ji ingantattun Hadisan Annabi (S) sun ayyana.


Ya ke ‘yar’uwa mai girma, idan har kin damu da mijinkin da yaranki, to lallai ne ki zubar da duk makaman yaki da zaman lafiya da kika daukarwa kanki. Shin kin san cewar wannan munanan dabi’un da kika dauka za su iya rusa miki gida gabaki daya su kuma tarwatsa maki iyali ki kuma rasa duk wani farin cikinki daga karshe ki zo kiyi nadama a lokacin da ba za ta yi maki amfani ba?


Idan ba kya jin tsoron haduwa da mahaliccinki ba ki tausayin rayuwar yaranki da kike neman ki yi masu illa? Kin san cewa duk gatan yaro idan bai tashi a tsakiyar iyayenshi biyu ba sai kin same shi da wani nakasu sabanin yaron da ya taso a gaban iyayensa biyu? ‘Educationist’ ma sun fada acikin matsalolin da ke sawa kaga yaro sauran sa’o’insa a aji sunyi masa zarra, akwai rashin jituwa tsakanin iyaye da kuma rabuwan aure [separation] wannan nasawa komai kokarin yaro ya koma baya.


Yar’uwa mai zai hana ki sawa ranki hakuri ki rungumi rayuwar yaranki ki sauke nauyin da Allah (SWT) ya dora maki na basu tarbiyya, su kuma yi rayuwa ta jin-dadi da walwala kamar ko wane yaro mai gata. Idan kika yi hakuri komai na rayuwan duniyar nan mai wucewa ne babu wani abu da zai dawwama, sannan gashi babu wanda ya san hakikanin lokacin tafiyarsa. Idan kika kasance kina cikin wannan yanayin Allah ya dauki ranki don Allah mai zaki fada a gaban maliccinki. Idan kuma ba ki mutu ba, to aurenki na iya mutuwa, da rabuwan aure ki fara ganin sakamakonki tun anan duniya, domin shi al’amarin aure tun a nan duniya a ke gane azzalumi a cikin ku.


— Daga littafin Marigayiya Wasila Ahmad (Ummin Sajjad), wanda ya rubuta tun a shekarar 2015, sai dai Allah bai nufi an Wallafa shi ba har sadda Allah Ya yi rasuwarta.


Allah Ya jaddada mata rahama da jinkai.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post