_Real Nusaeberty.
5th-Oct-2022.
Mafiya yawan mutane idan akace aikin “Media” abun da yake fara zuwa musu shi ne Ɗaukar Hoto 📸 a wajen taro, Alhali wannan ba shi kaɗai ba ne aikin (media) ba, yana daga ciki amma akwai fannoni dayawan gaske wanda aikin “Media” ya ƙunsa, wasu kuna iya gani a zahiri wasu kuma bakwa iya gani wasu kuna iya sani wasu ba ma lallai ku iya sani ba.
Wasu “Brothers” ɗin mu akwai waɗan da suke ganin céwa aikin Media ga Matan Aure sam bai dace ba a tunanin su, sabi da wasu dalilansu ko nace ra'ayinsu. To Sai muce to idan a tunanin ka aikin Media ga matan Aure bai dace ba to a Addinan ce fa? a Tafiyan Harka Islamiyya fa? shin ya dace ko bai dace ba? anayi ko ba'ayi? idan anayi mai yasa Su malam (H) basuyi magana akan rashin dacewar sa ba? idan muka koma ta ɗayan janibin Sai muce to Mai yasa Wasu Harisawa mata (Hurras) suke fareti wasu hadda ƴa’ƴansu ma? ko su Sayyid basu san da hakan bane tun tsawon lokaci har zuwa yanzu? Idan muka juya fagen Amawa waɗan da basu da hadafin da muke dashi me yasa wasu matan Auren da Aurensu suke aikin Media ko Jarida?
Nasan zaku cemin ai bai kamata mace tana da lalura na Juna (2) wato ciki ta fito gaban Al'umma tana Aikin media ba, na'am sai muce muku To ai da kunya ma ace mace tafito gaban jama'a tana ɗaukar hoto a matsayin aikin media amma tambaya.. Shin zata Tabbata da cikin har ƙarshen rayuwarta bata Haife bane kokuma zata haife? idan har zata haife to ai kunga zata iya cigaba da aikin median ta yadda ta tsara wa kanta... wata ma yaron da ta haifa ɗin nan gaba tana zaune a gefe guda shi zata aika yaje ya ɗauko mata Hoton ya kawomata tayi aikin da Zatayi, kunga kenan anan gurin kalmar “Birruhi wa Dammi” ya fito kenan ko, wato munce Zamu taimaka da jininmu dukiyarmu da dukkan abin da muka mallaka, in har ba yaudarar kanmu mukeyi ba...
To Abin da muke so muta ne su fahimta shi ne akwai matayen Auren da suna da basiran da zasu bada gudummawarsu ta fannin Media batare da ma sun fito sun fito gaban Al'umma sunyi Hoto ba, wata ma tana daga cikin gidanta zata iya bada tata gudumawar ta fannin Median Kuma. dan haka ƴan uwa maza idan abu baiyi daidai da ra'ayinka ba bai kamata ka dinga aibata abun kana nuna kaman haramunne yin hakan ba, idan bazaka iya barin matarka tayi ba bai kamata kuma ka raunata waɗanda zasu iya yi ba. Ba lallai ne sai abu yazo da ra'ayinka ko abinda kake so bane daidai ba, kuma dan bazakayi ba sabida ra'ayi ba shi zai baka damar ka aibata wacce taga zata iyayi ba.
Yana da kyau ƴan uwa muji tsoron Allah, kowa da yadda yaga zai iya bada tasa gudummawar a wannan harƙar kuma kowa nayi ne akan hadafi guda ɗaya na neman yardar Allah... kuma tafiyar nan babu inda akace baza'ayi da mata ba tunda ba yaƙi mukeyi ba, Fatan Allah ya wuce mana gaba. dan Allah ku ƙarfafi matayenku🌹🙏🏻