Malama Zinatudin Ibrahim Da 'Yar'yanta Shida [6] da Azzaluman Nigeria Suka Raba ta da su a 2014 Zuwa 2015..!!!



              ..El-Misawyy..

Wannan Baiwar Allah ta sha jarabawa iya jarabawa irinta Annabawa da Manzonni, yayinda ta Rasa 'Ya'yanta Shida dukkaninsu Matasa kuma mazaje ne mataimaka a gareta, sannan malama Zenatuden ta Rasa su ne, ta hanyar kisan kai, kisa na rashin tausayi.


 Bayan kisan 'Ya'yanta da Aka yi Sannan aka tsareta Shekaru Biyar da watanni Bakwai da Muggan Raunuka a jikinta na Harbin Da Sojojin Nigeria Suka Rika yi Mata, wanda har zuwa yanzu Masana lafiya ke cewa, tana bukatar duba lafiyarta na gaggawa, sannan sun ce har yanzu da Akwai Harsasai a jikinta tun bayan Harbin da Sojojin kasar nan Suka rika yi mata da maidakinta(Malam Zakzaky).


An fara kashe mata 'Ya'ya Uku ne tun a shekarar 2014 a Wata Muzahara ta Nuna Goyon bayan Palasdinawa a garin Zaria, wanda Sojojin Nigeria Suka Dirar musu da kisa, nan take aka kashe mutane 34 Ciki har da 'Ya'yanta uku, Ahmad, Hameed Da mahmoud da aka kashe su Ta hanyar Caccaka musu Wuka a jikinsu daga bisani Sojojin Suka Bude musu Wuta suka kashe su.


Sannan Sai Shekarar 2014 Sojojin Kasar Suka Sake Afka wa Almajiransu a garin Zaria, a ranakun 12, 13 da 14 Ga watan Disambar 2015 wanda aka kashe musu Mutane fiye da dubu daya, ciki har da 'Ya'yanta Guda uku, Aliyu hydar, Humaid da Hammad, wanda Aka kashe su a gaban idonta kisa na gilla da rashin tausayi.


Hakika Wannan matar ta Cancanci Zama Gwarzuwa abin koyi ga dukkanin Mata da Sauran 'Yan Gwagwarmaya ta hanyar  Nuna Juriya da dakewa akan Tafarkin Allah ta'ala, malama ta zamo Kwafi na sayyeda Zainab(As) a wannan Zamanin nan namu da ta nuna Dakewa da Juriya ga Dukkanin masifofin da ya Risketa.


Muna Rokon Allah ta'ala ya kara mata Sabaty, juriya da dakewa a wannan Tafarkin.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post