LABARI DA ƊUMI-ƊUMI: za a gudanar da Zanga-zanga nuna goyon bayan Shaikh Abdulja bar: ana sanar da magoya bayan Manzon Rahama ( S ) gobe Juma'a

 


Gagarumar Zanga-zangar Nuna goyon bayan Shaikh Abduljabbar; Za Mufito Domin Nuna Goyon bayan Adalci: Ƙungiyar Masoya Manzon Allah (S.A.W)

Ƙungiyar Masoya Manzon Allah S.A.W tare da haɗin Guiwar Matasan Ashabul-Khafi Muna gayyatar Ɗaukacin Masoya Manzon Allah S.A.W Zuwa Zanga-zangar Lumana domin Nuna goyon bayan Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara, Tare da Yin Allah wadai da Yanke masa Hukuncin kisa.

A Fahimtar Mu Lallai Wannan Hukuncin da Mai Shari'a Sarki Yola Ya Zartar Zalunci ne, kuma muna da Haƙƙin Mufito Mununa ƙin amincewar mu kamar yadda kundin tsarin Mulkin Najeriya ya Tanadar.

Za'a fara Gangamin ne daga Babban Masallacin Juma'a dake jikin Gidan Mai Martaba Sarkin Kano Dr Alhaji Aminu Ado Bayero a gobe juma'a 16 December 2022 da karfe 09:00 Na Safe.

wanda yaji ya sanar da wanda baiji ba, Allah Ya Taimake mu Ya Ba mu Nasara.


Sa Hannu:

Ahbabu Rasulullah (S.A.W) 

Matasan Ashabul-Khafi

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post