[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Harkar Musulunci ƙarƙashin Jagorancin Maulana Shaikh Ibraheem Zakzaky, ta nemi a saki Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara, cikin Gaggawa kuma ba tare da wani Sharaɗi ba.
A wata sanarwa da suka fitar wacce suka rabawa maneman labarai a yammacin Laraba, wacce take ɗauke da sanya hannun Halima Aliyu, ta ɓangaren Dandalin Ɗaliban Harkar Musulunci.
Sun kuma nemi duk me da al'umma tare da dukkan masu hankali da su sanya baki su shiga tsakani domin malamin ya samu ƴanci daga ɗanyen hukuncin Kotun Kano.
Sanarwar ta bayyana Shaikh Abduljabbar a matsayin wani mutum me ƙoƙarin kawo gyara a wannan al'umma kuma ɗan Shaikh Nasiru Kabara da ake girmamawa a Kano, Najeriya da kuma Afrika ma baki ɗaya.