Kwadayi da Buri..!



@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 


Kwaɗayi da buri mai yawa, yana janyo da na sani a lokacin da ba zai amfani mutum ba, 

Mafi akasarin mu mata kwadayinmu Shi ke janyomana mushiga mawuyacin hali, Dama kuma ita duniya in kanemeta takowace hali zaka sameta, idan har kasameta ba ta hanyar Allah da Annabi ba, Shakka babu wata rana Saita horar da kai.

Baba ''YAR'UWA,, Ga wanda yake sonki Sabi da Allah Amma da zaran kinga wani me kudi yazo gunki tsabar butulci da kwadayi, Sai ki juya wa wancan da yake sonki da gaskiya da amana dan bashi dashi, ki dawo gun shi wannan me kudin da bakisan ta wace hanya yake Samun kudiba, HALAL or HARAM, bai damekiba matukar zaina wankeki da Naira, Ya Saya miki kaya na alfarma, Waya na kece taro, Ya fiddake kunya a gun qawaye kin zama big girl, Girman Kai da jiji dakai sun qaru. 

Da za'azo afadamiki aibinsa awannan lokacin cewa zakiyi hassadace ake miki dan zaki samu gidan hutu. 

Gaba daya idanuwanki sun makance akanshi, Alhali shi baima san kinayi ba, Dan dama can ba sonki yake ba, ba dan Allah yake tare dakeba, Mebi dan diri/surarki, ko dan kyan fiskar ki, kode dan wani Abu dayayi kama da wannan da ya gani ajikin ki.

_KWADAYI MABUDIN WAHALA_

Ta daya bangaren kuma, Wasu iyayen su suke ingiza 'Ya'yansu, Kaji Uwa tace Ki kawomana Mai qashin arziki kar ki kuskura kikawo Mai qashin tsiya gidannan, To kajifa, talaka take nufi, wai talakane me qashin tsiya. 

Masu irin wannan dabi'ar, Basu damu da bincikar 'Yar tasu ta ina take samun kudi,? Sana'ar me takeyi, l? Wayake bata?!

Duk baida mesuba Domin su din ma Kwadayayunne

Yayin da me qashin arzikin yazo neman 'yar su, babu bincike ba komai Kaji sun dau 'yarsu Sun bashi, har suna alfahri 'yarsu tayi goshi tufar kalla, Basu damu da Sanin Asalinsa, Nasabarsa, da tarbiyyarsa,da kuma riqon Addininsa ba, Su dai Sun samu gurin hutu aci arziki kawai malam,

'YAR'UWA" Ki sani Alokacin da ya gane ke Kwadayayyace Wato ke Mayyar kudice, to sai shima ya bijiromiki da wata buqata tasa, kuma dik hanyar da zaibi ya ga ya biya buqatarsa to zaibi, dan cikar mummunar Qudirinsa, akanki, tinda tinfarko badan Allah ya sokiba kece kawai baki ganeba saboda abin duniya ya rufe miki ido, 

Kinga ko bazayyiwu yayita asaran kudinshi akanki haka kawaiba, kede in Allah ya soki ki ankare tin da wuri, in kuma kudinne ya rudeki sai ki fada tarkonsa{YA ILAHEE}

Kinga ke kikaja wa kanki, kuma tin farko dama angina soyayyar ne ba bisa koyarwar addinin musulunci ba. 

Dan haka muji tsoron ALLAH, ki sani ba komai bane acikin wannan duniyar face rudu da yaudara, Dan haka idan kika zamo mai yawan kwadayin abin duniya da rashin godiyar Allah to tabbas zaki dawwama cikin WAHALA da NADAMA duniya da lahira. 

'YAR'UWA" Idan kin yi hakurima arzikin da Allah ya raba aranar Allah zai baki, basai kin nema ta haramtaccen hanyaba. 

''YAR'UWA" Kisani cewa mafi akasarin "MAZAN" da suke yawan kashe maqudan kudi wa "MACE" ba dan Allah sukeyiba, Sai dai in sunga cewa akwai abinda suka hango wanda suke tinanin zasu samu daga gareki, {Qalilanne acikinsu masuyi sabida Allah acikin su} 

Na'am, (IHSANI) ga Masoyiya abu ne mai kyau yana kuma qara danqon qauna, Amma kar ya wuce misali kuma abi ta hanyar da ya dace, Idan har aka samu akasin haka to zai iya zama sanadiyar lalacewar tarbiyyarta. 

''YAR'UWA" Kisani cewa, idan ya bata miki rayuwa ya gama cutar dake har abada, Ba kuma aurenki zayyiba, kuma ma koda ya aureki daga ke har iyayenki ba ganinku da kima zayyiba, Sai kin gwammaci da zaman gidansa gwara miki prison, Saboda Wahalhalu da takura da kuma bacon ran da zaki yi ta fiskanta daga gare shi. 

Kinga bai kamata ki tsaya bata lokacinki akan mutumin da baisan yadda zai kare mutunci da martabarsa ba, bare kuma ya kare miki naki. 

KIRA NA A GAREKU MAZA MASU IRIN WANNAN MUMMUNAR 'DABI'A. 

Kuna amfani da rauninmu na mata Kuna cutar mana da rayuwa. 

Ku sani 'Ita 'Ya "MACE" tamkar Uwace ga dikkanin da "NAMIJI" Domin acikin cikin "MACE" Allah ya halicceka Kuma Macen nan da ka raina itace dai ta raineka, tajure Wahalhalu da dik wata nau'i na qazantar ka, Bugu da qari wannan 'YA "MACEN" ta zame maka Nutsuwa, (matarka) , Amma ka rasa wacce zakaci zarafinsa sai 'ya "MACE" Uwa. 

To Wallahi,bazaka taba goge sunan Mahaifiyarka daga jinsin mataba, dan haka aduk lokacin da kanemi kaci Zarafin 'ya "MACE" farko ka tina da Mahaifiyarka, Shin in ka aikata hakan kayiwa kanka da Mahaifiyarka adalci amatsayin ta na 'Ya "MACE" ?!

"'DAN'UWA" Ya Kama ku zaku tayamu kare mutuncin mu ba ku tayamu watsar dashiba, 
Idan ka kalli "MACE" tana kuka, ka rarrashe ta tamkar 'yar cikinka, ('Yar da ka Haifa)

Idan kaga wasu na gogarin cin zarafinta kamata kallon "Matarka" Ma'ana kai kokarin kwatar mata 'Yan cinta tamkar yadda zaka tsaya wa "Matarka". Nasan idan akace wane ya taba jikin matarka ko ya mari matarka, to ya zakaji aranka,?! Ai sai inda qarfinka ya qare, wajen kwatar mata hakkinta. 

Shin yanzu baka tinanin wacce ka lalata tazo tazama silar lalacewar 'Ya ko dan da kahaifa ?!koda baka da aure ai zakayi kuma zaka haifu, 

- Shin Yanzu baka tinanin wacce ka lalata tazama silar ya duwar fasadi aduniya?! Wake da al'haki kan hakan?! 

To bari kaji, dik abinda kayiwa 'yar wani ko Qanwar wani ko matar wani ko Mahaifiyar wani, to wlh sai anyiwa naka, komai killacesu da kake, Dan bakafi Allah wayoba

Ya kamata dik abin da zamuyi musa tsoron ALLAH, damin Allah na ganin dik abinda muke aikatawa, koda muna cikin rami ne, mu rinqa tina duniya ba matabbata bace malam.

Allah Yasa Mudace.....


SAUKE APPLICATIONS DINMU A WAYAR KA YANZU DOMIN SAMUN AYYUKAN MU AKOWACE RANA. GA APPLICATIONS DINNAN 👇👇👇👇


Kasancewa Damu a Shafin mu na Telgram 👇👇


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post