"Kusan awa shida muka kwashe Muna binne gawawwakin a babban rami da muka tona, don mun fara ne tun ƙarfe Sha biyun dare har zuwa ƙarfe biyar da rabi na ranar 14/12/2015.

 




KUN TUNA WANNAN KUWA?


Inji Namadi Musa (DG. Kad. State interfaith) 

da Balarabe Lawal (SSG Kaduna state)


 Sun bayyana haka ne Lokacin da suke bayyana yadda suka binne gawawwakin 'Yan uwa 347 a rami ɗaya waɗanda gwamnati ta kashe a waƙi'ar Zaria 2015.


Sun faɗi cewa sun yi amfani da Motocin Tipper ƙirar Marsandi mai cin ton shida wurin kwaso gawawwaki 191 daga Asibitin shika.

Sannan sunyi amfani da Manyan motoci guda 3 wurin kwaso gawawwaki 156 daga Depot Zariya.

Kuma Sojoji 40 ne suka raka gawawwakin.

Ƙarƙashin Jagorancin wani Major


Sun karanta wannan rahoton ne a ranar Litinin 11/04/2016 gaban kwamitin da Nasuru Elrufa'i ya kafa (JCI) ƙarƙashin Justice Lawal Garba don binciko musabbabin abinda ya faru.

Babban abin tashin hankali akan wannan ɗanyen aikin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta Jagoranta shi ne Akwai 'Yan uwa Masu Yawan gaske da suna da ransu amma haka aka tura su a rami aka binne su da ransu har suka daina numfashi😭


 SAƘONA ZUWA GA 'YAN UWA

Yakai ɗan uwa na mabiyin Sayyid Zakzaky (H)

Sau nawa ka taɓa kaiwa Yan uwan nan ziyara?

Ba wai sauran garuruwa masu nisa ba har a Kaduna akwai Wanda bai ma san wurin ba.

ashe bai kamata ace mun maida Wurin Kamar kasuwa ba saboda yawan ziyara?

Har sai Gwamnatin da kanta ta san ta tafka Gagarumin kuskure saboda yadda zamu riƙa jerin gwanon zuwa raya wurin daga garuruwa.

Bafa lungu wurin yake ba yana nan ana wuce Nepa bayan Camp ɗin Alhazai jikin maƙabartar Mando Kaduna.


Mu tuna bamu da wani wuri da muka tabbatar muna da 'Yan uwa Shuhada masu yawa haka Mai yasa muka gaza wurin raya wurin da Ziyara da sauran su koda kuwa sanadin haka Su Elrufa'i zasu cigaba da sheƙar da jinin mu?


Allah ya nuna mana ranar da zamu tono wurin mu ciro Yan uwan mu don yi masu ƙabari Irin na Musulunci.

Allah ka nufa mu ɗauki fansar ta'addancin nan Domin...

SAUKE APPLICATIONS DINMU A WAYAR KA YANZU DOMIN SAMUN AYYUKAN MU AKOWACE RANA. GA APPLICATIONS DINNAN 👇👇👇👇



2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Ya zanyi nayi copy

    ReplyDelete
  2. Ya Allah Ya Allah Ka Karbi Shahidanmu Mu Kuma Ka Bamu Sabati Su Kuma Mahukuntan Shedan Katsine Musu Albarka Ka Hadasu Rigima Da Jabara'il (As). Writted By Muhammadu Buhari Dalibi Zaria

    ReplyDelete
Previous Post Next Post