Kungiyar Dalibai Ta Bankado Munanen Kalmomi A Bukhari Da Muslim Wadanda Malam Abduljabbar Ya ke Ikirarin Korewa Annabi(S)..!

 




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


A wani bincike da kungiyar Islamic Intersectional Students Organisation (ISO) ta yi, domin na zari akan hukuncin kisa ta hanyar rataya da wata kotu ta yankewa Shehin malamin, saboda ikirarinsa na kore wasu hadisan karya da su ke ɗauke da cinmutuncin Annabi s.a.w a Bukhari da Muslim.  


Ƙungiyar me suna a sama ta samu nasarar fitar da sakamakon binciken da tayiwa laƙabi da "Nazarin Hoto", saboda temakawa mambobinta ɗaliban ilimi gano gaskiyar ikirarin Shehin malamin na korewa Annabi s.a.w wasu munanan hadissan da su ke taba mutuncinsa a cikin wasu littattafan hadisi.

A sanarwar da kungiyar ta fitar tana ɗauke da misalin waɗannan hadisan da malamin ya yi ikirarin cewa "dukda hadisan su na cikin Bukhari, amma ƙarairayi ne aka jinginawa Annabi s.a.w, kuma karyar ta na taba mutuncinsa, idan mu ka yi la'akari da munin aikin da ke cikinta."


Misalin munanan kalaman da su ka yi ikirarin barranta da su a wasu hadisan Bukhari su ne👇


- Ƙaryar cewa "Annabi s.a.w ya saka hannu ya kwaye cinyarsa", amaimakon rufe ta. Bukhari 371


- karyar cewa Annabi s.a.w ya yi zigidir, har kuskuren yin haka ya janyo masa faɗuwa sumamme. Bukhari 364


Nazarin Hoton yana ɗauke da hadisan cikin Larabci, Turanci da sharhinsu da Hausa.  


Abin lura anan shine gamayyar malaman duniya sun hadu akan cewa duk Annabi ma'asumi ne Kuma baya kuskure, sannan ya fi kowa kyawun dabi'a da hankali.

Wannan dalilin ne yasa babu ta yadda za'ayi a iya jinginawa Annabi wani aiki da ya sabawa kyakkyawar dabi'a, tunda a wajensu gabaki dayan Al'umma Allah ya yi umarni su koyi dabi'un girma.


Daga kungiyar dalibai ta ISO.


Me rahoto

Tijjani Abba.

3 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Allah ya karawa Annabi daraja

    ReplyDelete
  2. Babu Inda abduljabar yazagi annabi Kai tsaye akulun kare Martaban Annabi yakeyi chewa yayi anzagi annabi bashi yayi zagiba saboda haka dole asake duba da wanan lamari

    ReplyDelete
  3. Mlm Sarki ko yanzu yayi nasara saboda dole wasu daga cikin mutane zasuyi ta binciken gani irin wayannan hadisan na karya harsu gane manufarsa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post