Inji Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).
Yace: "An ce min cikin ‘yan siyasar ma akwai wani wanda yace ai sun ga uwar-bari ne, yanzu sun dawo siyasa, saboda ‘impression’ din da wadansu suka basu. Wato kamar mun ci wuyan tsiya ne, an kashe mana sama da mutum dubu, an rugurguza mana komai, yanzu mun ji ba dadi, mun ce to yanzu mun shiga siyasa. Nace to Allah Ya sauwake!
"Ni na san cewa ko mafarki mutum ya yi, ya ji ance Al-Zakzaky yace yanzu ya narke shi dan siyasa ne. Idan ya farka zai ce mafarkin nan ya yi masa karya. Abin nan da aka sanni a kai shekara kusan 47 da suka wuce a kan haka nake, kuma Insha Allahu a kai zan bar duniya.
"Yaushe ne duk bayan wadannan kuma mutum yanzu ya rasa hankalinsa? Yanzu don Allah idan mutum yana da hankali zai yi tunanin cewa abin da aka yi mana zai sa mu yi ‘surrender’ (mu mika wuya)? Me muke bukata? Mu bukaci mene? Har abada! Ai sun mana abin da ma in ma suna neman mika wuyan ne, sun san ba za su samu ba. Me ya rage wanda za su mana.
"Ballantana kuma ace mutum ya shekara 47 yana gwagwarmaya ba tsayawa, sannan kuma a sanadiyyar haka nan an kashe mutane sama da dubu, sannan an kukkule mutane, an cutar da su, ba abin da ba a yi ba, sannan kuma wai sai a ce mu yi me kuma? Me ya rage kuma? Me ya rage mana? Dan shekara 70 ya shekara sama da 40 yana Harka, sai kuma dan abin da ya rage masa, mutuwa ko yau ko gobe, ya ci mene a duniya?"
— Shaikh Ibraheem Zakzaky a yayin ganawarsa da 'yan Political Forum ranar Talatar makon jiya, 29/11/2022 a Abuja.