Ko Kunsan Annabi Isa Ya Kusa Bayyana ??



 Daga Sani Hamisu.


Malamai suna yawan yin bayani akan dawowar Almasihu duniya. Ranar Juma'ar nan da ta wuce sai na ji mai huduba yana bayyana alamomin tashin Alkiyam ciki kuwa na ji ya fadi cewa har da dawowar Annabi Isah duniya domin ya shimfida adalci a doran kasa.

Na gama nazari na da bincike na cewa, duk lokacin da ‘yan’uwan mu Musulmai wato Ahlul -Sunna, idan suka tashi bayyana alamomin tashin alkiyama basa fadawa mabiyansu cewa akwai dawowar jikan Manzon Allah Imam Muhammad Mahdi (A.F). Amma sukan ce; “akwai Bayyanar Yajuju Wa Majuju. Dawowar Annabi Isah, da kuma Taguwar Annabi Salihu.”

Na kasa fahimta wacce irin gaba ce, ko kuma na ce kiyayyar da take tsakanin ‘yan’uwana Ahlus Sunna da kuma bayyanar Imam Mahdi. Na ji da kunnena daya daga cikin Malaman Ahlul-Sunna wanda zan sakaya sunansa, yana bayanin akan Alamomin tashi Alkiyama, sai yake cewa a karshen duniya Annabi Isah  zai dawo kuma idan ya dawo zai yi fada ne da Kafirci. Sannan a lokacin da yake wannan yaki da kafircin ne, zai hadu da jikan Manzon Allah (A.S), su yi Sallah tare, har jikan Manzon Allah zai ce da shi ya wuce gaba ya ja su Sallah. Sai Annabi Isah ya ce wane shi dan Maryam ya ja dan Fatima Sallah. To a nan ne jikan Manzon Allah sai ya ja Sallah. Amma a nan abin da ya kasa fitowa ya fadawa mabiyan na sa cewa; wannan jikan Manzon Allah (A.S)  ba kowa bane illah Imam Mahdi sai ya boye yaki fadi. Su kuwa daga cikin daliban nasa ba, a samu ko da mutum daya wanda ya tambaye shi wane ne wannan ba.

To abin tambaya shi ne shin me yasa 'yan’uwana Ahlus Sunna baku son ku fito ku fadawa mabiyanku cewa akwai jikan Manzon Allah (S) Imam Mahdi wanda zai zo karshen duniya ya yi yaki da kafirci? Ko kuma kuna tsoron fada musu ne saboda kar su ce kun zama ‘yan Shi'a?

 Allah ina rokonka ka nuna mana gaskiya ka bamu ikon bin ta, ka nuna mana karya, ka bamu ikon kauce mata.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post