Ko Ka san Wadanda Suka Fi Zakewa Don ganin Bayan Mlm Zakzaky [h] da da'awarsa Musulmai Ne ....???

 


... Umar Hassan Gololo... 

Shi Buhari wanda aka ce zabensa Jihadi ne, kuma faduwarsa kamar faduwar Musulunci ne, shine yace Malam Zakzaky(H) Ya kafa Gwamnati cikin Gwamnati, kuma ya ga yadda budurwa take dukan kirjin General din soja. 

Shi kuwa El-rufa'i wanda ake kira Nasiruddeenil-Islam cewa yayi wai Malam Zakzaky(H) bai yarda Buhari Shugaban Nigeria bane kuma bai yarda shi Gwamna bane. 

Shi kuwa General Buratai cewa yayi anyi yunkurin hallaka shi a hanyarsa ta zuwa Gidan Sarkin Zazzau. 

Shi kuwa Brigadier general Sani Usman kukasheka cewa yayi wai an tarewa Buratai hanya har ma anyi harbe-harbe da bindiga a bakin Hussainiyyah Baqiyatullah. 

Shi kuwa korarren Sarkin Gargajiyar Kano Sunusi Lamido Sunusi cewa yayi an kafa Nigeria a tafarkin Sunnah ne ba Shi'a ba. 

Shi kuwa Garba Shehu cewa yayi ba ana tsare da Malam Zakzaky(H) bane, yana Protective Custody ne. 

Shi kuwa Lai Mohammed cewa yayi suna kashewa Malam Zakzaky(H) Naira Miliyan uku da rabi a abinci kullum. 

Ban kawo Musulman da suka rinka caje aljifan gawarwaki suna satar kudade har da yanke yatsa domin cire zobe ba. 

Ban kawo Musulman da suka rinka yin walima da murnar kisan dabbancin da aka yi mana ba. 

Ban kawo Musulmai mawakan da suka rinka yin wakokin yabon wadanda suka yi mana kisan dabbancin da aka yi a Zaria ba. 

Ban ambaci kidahuman mutanen da ake kira masharhanta da Miyagun Malaman fada da banzayen da ake kira masana harkokin tsaro ba. 

Sun yi karya sun yi sharri da kazafi, sun yi zagi da duka, sun yi kisa da rusa gidaje amma wace riba suka samu a Duniya, wace riba kuma zasu samu a Lahira? 

Shin Buhari zai bayyana ta'addancin Zaria a cikin daya daga cikin Nasarar mulkinsa? 

A dukkan sharrukan da aka yiwa Malam Zakzaky(H) da Almajiransa akwai guda da kotunan da Gwamnatin Buhari ta kai kara suka tabbatar dashi? 

Yanzu wanene yaci Nasara tsakanin Malam Zakzaky(H) da Buhari?

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post