KO JAMI'AN TSARON KASAR MU BA SU GOGE BA ?

 


...Darasi Daga Bam din 2010


...Daga Ina Matsalar Ta Faro?


Daga Danjuma Katsina 


Matsalar da kasar mu ta shiga na rashin tsaro, musamman a arewacin Nijeriya na sanya jefa zargi da suka a kan jami'an tsaron mu, musamman masu tattara bayanan sirri da masu aiwatar da tabbatar da tsaron.


Ana rubuce-rubuce cewa jami'an tsaron kasar kamar ba su da gogewa ko karancin kayan aiki ko kishi.


Na taba samun damar karanta wani bayanin tsaro da aka taba bai wa marigayi MD Yusuf (Allah ya jikan sa da rahama, ya kyautata bayan sa). Tun  da yake lamarin ya wuce shekaru 10 da faruwa, ina iya ba da wani bayani da na gani a cikin rahoton domin misali.


A shekarar 2010 bam ya tashi a Dandalin taro na Eagle Square da ke Abuja. Nan da nan kwararru a kan tattara bayanai a inda aka aikata laifi suka isa wajen suka tattara abin da suke bukata. 


Cikin awa 48 har sun gano wadanda ake zargi sun dasa bam din, amma babu adireshi ko lambobin waya, amma an gano wasu 'yan'uwansu.


Cikin kwana uku da faruwar lamarin an samu lambobin wayarsu da fuskokin su, a musayar sakon magana da aka samu har da yaushe za a cika mana kudin mu? Mu hadu waje kaza mu kammala tattaunawa da sauransu.


A tattara hujja da bayanai, jami'an tsaro suka nufi kasar da aka kera motar da aka yi amfani da ita. Daga can aka biyo yadda aka siyar da ita. Daga hannun wane zuwa wani. Sai ga shi ta fado hannun wani a birnin Fatakwal.


Cikin kwanaki an kamo mai aikin walda da ya kera wajen da aka ajiye bam din.


Cikin kwanaki an kammala tattara bayanan yadda suka shigo Abuja da inda suka suka har da gidan man da suka sha mai karshe.


Bayan kammala tattara bayanan da za su iya gabatarwa gaban kotu ta hanyar ayyukan asiri, cikin kwanaki kadan suka shelanta wa duniya wadanda suka kai harin. Yanzu haka duk suna tsare a kurkukun Nijeriya. 


Jami'an tsaron mu sun iya aiki, sun kuma san aikin. Sukan samu horo daga takwarorin su na kasashe duniya.


Ina matsalar take? Masu mulki na siyasa sukan yi amfani da tsaro don biyan bukatar kansu ta satar kudi ko biyan wata bukata.


Duk lokacin da za su yi wannan, sai su ki ba da cikakken goyon baya ga jami'an tsaro don su yi aikin su.


Za su iya shelanta wani abu gaban talabijin don 'yan kasa su ji dadi, amma za su ki tabbatar da maganarsu a hukumance.


A gwamnatin Buhari, babbar matsalar tsaro ta fara ne daga kisan kiyashin da soja suka yi a Zariya a watan Disamba, 2015.


A rikicin da aka kira sojoji da 'yan Shi'a almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky.


A wannan kisan na soja da suka auka wa 'yan Shi'a babu wata dokar yaki da aka yi amfani da ita, domin an kashe mata da yara.


Sauran hukumomin sirri na kasar nan ba da hannun su ba dari bisa, dari,soja suka tsara mummunan aikin suka aiwatar.

Hatta wasu hukumomin tsaro na soja sunyi adawa da aika aikan

Wasu manyan kasashen duniya sun tabbatar ba abi dokar yaki ba a abin da soja sukayi a zaria .

Shi yasa kafofin watsa labaran su da kungiyoyi kare hakkin Dan Adam nasu ke sukar abin da ya faru a zaria disamba 2015.

Marubucin nan ya karanta matsayar wasu kasashen akan mummunan lamarin 


Masana jinin dan'adam sun tabbatar babu yadda za ka zub da jinin yaro da jariri Allah bai yi sakayya ba.


Hakkin wadanda aka kashe a Zariya ba tare da wani laifi ba, musamman kananan yara da jarirai da mata da masu wucewa ke bin jami'an tsaron mu.


Tarihin duniya ya tabbatar a baya duk inda aka yi irin wancan kisan, sai Allah ya jarabci wajen.

Malaman addini sun tabbatar kashe yara  da mata na afkar da tsoro fitina da talauci.

Shi ya yaki yake da dokoki, ba Wanda bai dauke da makami ba yara ba mace ba Wanda ya juya baya ko yayi saranda .

Mutane nawa aka kashe a fitinar Zariya suna cikin wannan yanayi?

Ba daga lokacin bane, jami an tsaronmu suka shiga wani yanayi musamman ma sojoji?

Allah ya sawwaka ya kiyaye gaba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post