Kisan Kiyashin Buhari A Zaria!!!




Wajibi ne fara neman Afuwar gyauji, Kura, Sayaki, Zaki, Damisa, Kyarkeci, Gwanki, Bauna da sauran Namun Daji. Domin Aron sunanansu a kira wadanda sukayi aika-aikar Zariya dashi, cin zarafi ne garesu. Domin su cin danyen Nama Dabi'arsu ne, duk da haka basa cin Jinsinsu. 


Amma a Zariya an samu wasu Kaskantattu masu Jiki irin na Mutane sun Sha jinin Mutane, suna Ihu suna Al-fakhari. Duk inda aka taba yin kisan kiyashi a Tarihin Duniya, zaka ga wata Kabila ce ta kashe wata Kabilar da bata kauna. Amma bamda Karbala, kuma banda Zariya. 


Zariya taga aikin Ta’addanci da jahilci da Dabbanci a ranar 12-14 na watan Disambar shekarar 2015.


Tarihi ya maimaita kansa , Karbala ta sake maimaituwa. Jini ya sake kwarara, domin ya mamayi Tinkahon Bidiga, ya nade Hujjar Bullet, ya Turmuza Taurin Kan Azzalumai, ya goga Hancin Zalinci a saman kasar Jigawa.


A rana tsaka sojoji ‘Yan ina-da-kisa suka aiwatar da kisan kare-dangi akan Yan Harka Islamiyyah ta Nageriya, suka kashe fiye da mutum dubu (1000+), a Husainiyyah da Gyallesu da Darur Rahama, dama wajen Garin Zaria.


 Suka kona wasu da ransu, suka halbe Jariri, suka farke Al-aurar Mata da Wuka, suka halbi Ciki, Jinjiri ya fado suka Dambara mashi Halsashi, Motar yaki tabi saman Jikkunan wasu da Ransu, ta Markadesu. 


Suka ruguza Husainiyyah da Gidan babban jagora Sayyed Ibrahim Zakzky (H), wanda sojojin suka harba harbin kisa, amma Allah (SWT) bai basu damar kashe shi ba, sunyi sanadiyyar raunata wasu sassa na jikinsa, bayan sun kashe 'Yayansa, a gabansa, Kwanyar waninsu ta tarwatse saman Jikinsa, sun harbi matarsa Malama Zeenat Ibrahim, suka je har makabartar Darur–Rahama suka tarwatsa wurin, suka tone kaburbura, daga ciki har da kabarin wasu ‘Ya ‘yansa uku da suka kashe a sherkar 2014.


Duk wannan bai ishesu ba, suka wuce makwancin mahaifiyarsa Mai Daraja, suka ruguza, suka tone. 


Suka kuma tsare Malam tare da wasu magoya bayansa, babu beli babu zuwa kotu, na tsawon Watanni. Sannan a ka koma Kotu ana was a da hankalin raunana. Amma duk da haka saboda munin Dabbancin da suka yi, hatta Kotunansu sai da suka basu Rashin Gaskiya, bayan da Malam ya kaisu Kara. 


A haka suka bizne mutane fiye da dari uku da Arba’in (340+) cikin Rami daya, wasuma da ransu, suna rokon kada a binnesu da ransu, amma haka suka turasu cikin ramin, suka sa mota tabi ta kansu da kasa, ba tare da tausayi ba.


 Suka yita karairayi da Izgili da kage da Kazafi,, domin rufe wannan Aika-aika, amma Allah bai yadda ba, sai da ta bayyana ga kowa, domin ta zamo hujja a gareshi ko a Kanshi. 


 Bayan haka sun kama wasu suka tafi dasu bariki suka dinga gana masu Azaba kala-kala, sun ci mutun cin mata, sun ci zarafinsu, sun kulle tare take haqqin Yara. 


Sun aikata Dabbanci ko muce Ta'addanci wanda ba wani Al-kalamin da zai iya bayyana shi a Zariya.


Wannan ta’adancin Sojoji a zariya na tsawon kwana Biyar ya shafi sama da mutum dubu biyar (10,000+), akwai sama da dubu(1000+) da aka kashe, akwai Iyali Dari takwas da tamanin da bakwai (887) da abun ya shafa, an kuma samu matan da suka rasa mazajensu guda dari huda da saba’in da biyu (472), an samu marayu sama da dubu daya da dari tara(1900+), kuma an samu Jariran da aka Haifa sama da dari(100+), akwai dalibai sama da dari da cas’in (190+), an samu sama da mutun dari uku (300+) masu raunuka. Bayan wannan akwai tarin dukiyoyi da aka bannata wadda a kiyasce tafi biliyan Biyar. 


Duk wannan ta’adancin da sukayi a Zariya, da wanda suka yi a Sauran Garuwa, Musamman a Abuja, a Lokuta mabambanta, bai ishesu ba har yanzu, suna nan suna bi garuruwa suna ta kashe ‘Yan Uwa, kamar irin su Funtua da Kaduna, Kano, Jos, Katsina, Sakkwato da sauransu.


Duk wannan anyi shi da tuhumar tare hanya, a wajen hukuma, da kuma zagin Sahabbai, a wajen Kidahuman Malamai, wadda Labewa ce kawai bayan Karsana domin halbin Barewa. Da yake Ragage ne, gashi sun yi kisa Amma sun Kasa Fitowa Fili su fadi Dalilin Kisan. Sai suka labe da Karerayi irin na maras Hujjah. 


Banu Umayyah na yau wato gwamnatin Alu Sa’ud (wadan da suka fi dace wa da sunnan (Alu salul), wadda take Mummunan Kisa wa duk wani wanda bai yadda da danniyarsu ba, ko yake Adawa da kawarta Isra’ila. 


Sune Suka zuga gwamantin General Bukhari Zankalelen Mugu ya aiwatar da wannan Dabbanci. inda ya zamar musu Karen farauta, su suna kashi a can gida saudiyya, shi kuma yana kashewa a nan Nageria, tare da goyan bayan wasu Gwamnoni, kamar su Nasir El-Rufa’i(gwamnan Kaduna) da Ganduje (Gwamnan kano) da sauransu. 


Tsoronsu shine kada Addinin Allah ya nshe Ragamar Iko a wannan Kasa, kamar yadda yayi a shekarun baya. Sai suka aikata abunds zai gaggauto da abunda suke tsoro, saboda Jahilci da Wauta. 


Shamsudeen Hassan

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post