A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, CBN ya ce a yanzu ɗaiɗaikun mutane za su iya cire kudi har naira 500,000 yayin da kamfanoni kuma za su iya cire naira miliyan biyar duk mako.
Wannan sabon matakin na CBN na zuwa ne kwana 15 bayan fitar da dokar farko da ta ƙayyade yawan kuɗaden da mutane za su iya cirewa daga bankunan a duk sati.
Tun da farkon CBN ya ce ɗaiɗaikun mutane za su iya cire naira 100,000 ne su kuma kamfanoni za su cire naira 500,00 ne kawai a duk mako.
Sanarwar ta ce: “Wannan umarnin ya shafe na baya da ak fitar ranar 6 ga watan Disamban 2022, kuma zai fara aiki ne a fadin ƙasar daga ranar 9 ga watan Janairun 2023.”
Hakan dai na zuwa ne bayan da CBN ɗin ya sha matsin lamba daga ƴan ƙasar da dama ciki har da majalisar wakilai.
A cikin sanarwar wacce CBN ya aike wa dukkan bankuna da hukumomin da e hada-hadar kudi a ƙasar, babban bankin ya ce ya sauya matakin nasa ne bayan da ya samu bayanai daga masu ruwa da tsaki da yake mu’amala da su bayan matakin farkon.
Sai dai duk da haka CBN bai janye matakin cewa duk wanda zai cire kuɗaɗen da suka fi hakan yawa saboda dalilai masu ƙarfi ba, to sai an caji kashi 3 cikin 100 ga ɗaiɗaikun mutane da kuma kashi 5 cikin 100 ga kamfanoni.