KASAR IRAN: ta kama yan leken asiri a wani bayani da ta fidda.



------------------

Jumhuriyar musulunci ta Iran

 ta yi babban kamu.

---------------

A wani bayanin da ta fitar yau Alhamis, Ma'aikatan leken asirin Iran (MOIS) ta sanar da cewar,  jami'anta sun samu nasarar cafke shugabannin wasu kungiyoyin 4 dake yiwa kungiyar MOSSAD aikin tattara bayanai da kuma aiwatar da ayyukan ta'addanci a Iran. Bayanan sun kara da cewar MOSSAD ta yi cushen wakilan nata ne domin su saje cikin wadanda suka tayar da tarzoma a kwanakin baya a Iran domin gabatar da nasu shedancin ta hanyoyi daban daban, amma kuma tun shigowarsu kasar Jami'an MOIS din ke bibiyarsu har zuwa ranar da aka cafkesu.

Binciken farko ya nuna yadda suke hurda da wasu mutanen dake kasashen turai (Yan MOSSAD) domin batar da sawunsu a cikin Iran. 

Ma'aikatar ta bayyana cewar tana cigaba da tatsar bayanai kuma zata yi karin haske nan gaba kadan.

----------

Nasir Abu Muhammad

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post