[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Nasir Isa Ali
Lokacin da Umayyawa suka so kashe Imam Ali (as) sai suka yada farfagandar cewar Imam baya sallah kuma baya yin azumi da wankar janaba. Umayyawa sun kwashe shekaru suna yada wannan farfagandar har sai da dayawan mutane suka yarda da abin da suke fada. Amma da Allah ya tashi wanke imaminsa sai su Umayyawa suka yi kuskuren kashe Imam a cikin masallaci yana sallah, don haka sai labari ya bazu cewar an kashe Imam Ali a cikin masallaci yana sujuda. Wannan ne yasa musulmi da dama suka fahimci cewar ashe banu Umayyata sharri da karya suka yada a kan Imam.
Lokacin da zasu kashe Imam Husaini haka suka rika yadawa cewar wai yayi wa Amirul muminina bore yayi tawaye wq addinin kakansa Muhammedu zai koma Kufa domin ya dawo ya yakesu, a haka aka cinye kwakwalen miskinai da wawayen gari da wannan farfagandar, amma da Allah ya tashi tona musu Asiri sai aka kashe Imam a dajin Karbala sannan aka daure iyalan annabi tare da kan Imam zuwa Damashq wajen sarki Yazidu (la) wannan ne ya sa mutane suka fahimci zalincin da aka yiwa Imam da iyalan Annabi.
Haka zalika lokacin da ake son a kashe mallam Zakzaky (H) da almajiransa sai aka kirkiro sharrin wai almajiransa sun tare wa wani hanya sannan sun nemi halaka shi.
Amma da suka yi kuskure sai suka yi kisan kiyashi suka bi malam har gidansa suka harbe shi da yaransa da iyalinsa. Sannan suka je suka binne mutane ciki har da masu rai. Amma da aka je kotu sai asirinsu ya tonu cewar mallam bai aikata laifin komai ba, kuma dole a biyashi diyya.
Haka da suke son su kashe mallam Abduljabbar NK sai suka kirkiri karyar wai ya zagi annabi suka kai shi kotu suka yanke masa hukuncin rataya. Amma da Allah ya tashi tona musu asiri sai ya baiwa mallam Abduljabbar ikon yin irin abinda sayyada Zainab tayi bayan kashe Imam Hussain a gabqn Yazidu (la) sai mallam Abduljabbar ya fayyace abinda ya faru cikin jarumtaka da izza sannan yayi musu MUQAWAMAR da ba zasu taba mantawa ba a rayuwarsu.
Mu karanta wadannan ayoyin na kasa muga inda mallam Abduljabbar ya samo sunan matifiyarsa da kuma madogararsa. Ya Allah ka baiwa mallam Sarki sabati a duk inda yake.
Nasir Abu Muhammad