@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
Yawaita mafarki yana Yawaita Bacci. Hadama da Zari kayan Mayunwaci ne. Haka yawaita Buri ba tare da Sa'ayi da Hubbasa domin tabbatuwarshi ba, Alamar Ragganci ce, kuma Siffar Kasalah ce. Ai shi Holokon Hadari baya Ruwa. Idan kaji an ce wannan Hadarin Gagarumi ne, to sai da yasha kwaram, kafin ya Girma. Dole sai da ya hadu da wasu kananan Giragizai, idan suka cure, suka dunkule waje Daya, Sannan za'a kirashi Mamako.
Sanya aikin Gara ce, haka Labaru da 'Yan Kisoshi aikin Rago ne. Da kagaji yana ambaton wadanda suka tashi suka dage kuma suka yi Nasara, har yana Burin zama irinsu. Kafin ya burgeka, har ka fara yabonshi, ka fara dubin a ina ne yake maganar?
Idan a Teburin mai Indomei da Shayi ne, ko Dandalin Majakisar zaman banza, ta cikin kwana da Layin Shiyarsu, ko gidan kallon Wasa, to idan ba'ayi hattara ba, za ka Tarar katon Raggo ne, Makwadaici, Matsoraci, wanda baya iya fita Comfort zone domin haqqaqa Buri. Irin wannan baya iya fidda Suhe daga Wuta. Barshi dai wajen iya boye Hassada.
Mai aiki bayada time din Surutai, tulin tsaunin da ke gabansa ne kawai yake kallo, labarin Nasarorin wasu ba zai dameshi ba. Yaya za'ayi shi yayi Nasara shine zance a wajensa.
Batun "tare muka taso dashi", " tare aka mana Ka iya", "ai classmate dina ne", " a gidanmu suka zauna", " ni na fara sayo mashi Kalma ko Riga", " shekara Ukku muna kwana a Daki guda", " Dan Garinmu ne, ko Dan Uwana ne", da sauran ire-iren wadannan Sumbatun, duk Alamomin ne na Wanda Yaki ya Cinye, kuma tuni ya dade da ansar defeat a fagen Fafatawa.
Gwarzo shine wanda Labarinsa a kullum baya wuce " ai ina nake yanzu", " ya za'ayi na kai inda zani", "mene ne Matsalar da ta hana ni kaiwa", " ya za'ayi na sha gabanta na ci gaba da Tafiya", ba yaushe wane ya kai ba.
Akwai bukatar Hausa ta zanca salon Tunaninta game da Sulukinta na Rayuwa. Musamman Matasa, musamman masu Kishin Addini.
Aiki ake Bukata ba Labarun aikin wasu ba, da himma ake Tafiya ba da Mafarki ba, da Azma ake Kaiwa ba da Kasalah ba.
Sai an auri Juriya, an yi Amintaka da Hakuri, an kauda Kai daga Jahilai, an Rungumi Gaskiya, an bar Bacci, an keta Duhun Dare Sannan a wayi Gari alhali an isa Gari.
Matakin farko shine Falkawa, Sannan Dogara ga Allah, mika masa Linzamin Dokin, Sannan Zabura, Sannan Himma, Sannan Azma, Sannan Dagiya, Sannan Juriya, Sannan Hakuri, Sannan Hakuri, Sannan Hakuri, Sannan Nasarorin.
Shamsudeen Hassan