[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
1 . Sayyida Faɗima (a.s.) ta samu tambarin shahada , wanda muƙami ne na Aƙida da Ma'asumi yake Siffantuwa dashi kamar Ilimi Ladunni.
2 . Da dakewa da juriyarta wajen fuskantar Azzalumai ta sunnanta wani wajabci daga cikin wajiban Shi'anci , shine wajabcin bada kariya ga Imamin zamani .
3. Rukunan Shi'anci guda Uku ne : Aƙidar da ta ginu akan dalilai na Hankali da Nassoshin Shari'a , Hukuncen-hukuncen Fiqhu da aka rawaito daga Ai'mmatu Ahlil baiti (a.s.) , sai kuma Mazlumiyyar da take ƙunshe da sadaukarwa da bayar da rai fansa dan kare gaskiya da Ahlinta .
4 . Jini na Farko da yayiwa Shi'anci fentin Mazlumiyya da sadaukarwa Sannan ya assansa rukuni na uku daga cikin rukunan Sha'air na Shi'anci shine jinin Sayyida Faɗimatuz Zahra (a.s.) .
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey