WASU DAGA WADANDA MUKA ZAUNA DA SU SUN JE SUNA MAGANGANU
To da ma an tsaya a nan, da hanya guda ne, za a iya fitowa fili a ce ba a san wadannan abubuwan da suka kira shi ko Shi’a Political Forum, ko All Shi’a Political Forum din ba, ko ba a san wadannan mutanen ba, ko kuma duk wanda ya yi hulda da su ya yi ne ma kansa. A’a, sai ya zamana kuma wasu ba’adin wadanda aka zauna da su suma sun je suna maganganu.
To ni na san in dai an yi ‘meeting’, in dai sunansa ‘meeting’, ban taba sanin in an yi ‘meeting’ sai ka je kuma ka tara mutane kace ai an yi zama ga abin da aka yi ba. Saboda ko ba komai ba an aike ka da sako ne aka ce yanzu ka je ka fadawa mutane ba. Mu ne muka yi ‘meeting’ muka tattauna abubuwa. Sam bani tunanin cewa wani zai je yace gashi an yi ‘meeting’ kuma ga abin da aka tattauna ba.
To amma wani sai ya zama mutane ya tara yana ta musu bayani; an yi kaza, an yi kaza, an yi kaza, Malam yace kaza, Malam yace kaza, Malam yace kaza. Sai kace shi Malam din bashi da bakin magana ne, sai wannan ne zai je ya fada wa mutane abin da Malam yace, ko kuma an aike shi.
Na san ko da ma zai yiwu ace shi Malam din yana da abin da zai fadawa mutane, ba zai yiwu ya zama wadansu ne zai fada ma sai su je su fada ba. Saboda yanzu akwai hanyoyin sadarwa daban-daban, wanda za a yi magana da mutane kai tsaye idan ana so a yi. To amma na ji shi wannan Malam yace din ya yawaita. Har da kuma abin da suka faru da wanda basu faru ba.
Alal misali, a cikin abin da yace, yace an shirya wasu wakilai wadanda za su ga lokacin da ya dace sai su fadi wadanne ‘yan takara ya kamata a mara musu baya, wai su ne za su ga in lokacin ya yi. Ni kuma na tabbatar da cewa ba wannan maganar a cikin abin da muka yi magana a nan wajen, ba wani abu mai kama da haka nan.
To, banda wannan sai kuma wasu suka je suka yi hira da gidan rediyo. Mai hira da gidan Rediyon yace, shi ‘Principle’ baya canzawa amma ‘policy’ kan canza, to tunda ta kai ma ga kaga Jagora ma da kansa ya kafa Dandalin Siyasa, to kaima ka san abin da wannan ke nufi. Ma’ana (yana nufin yanzu) ‘Policy’ ya canza.
NA TABA YIN BAYANI A KAN ‘POLICY’ DA ‘PRINCIPLE’ A BAYA
To, na san tun wani lokaci na taba magana, tun a Islamic Center (a 2009), tun a lokacin na yi wata magana, da Hausa nake magana, amma sai na kawo wasu kalmomi ‘musdalahat’ da Ingilishi, nace ‘principle and policy’, nace shi abin da ake nufi da ‘principle’ shine ginshiki –abin da aka doru a kai, wanda yake idan an rusa shi komai zai rushe. A kan Ginshiqi ake dora abu, idan ka rusa ginshiqi kamar ka rusa abin kenan, saboda a kanshi ya doru.
Wannan shi abin da ake ce ma ‘principle’ shine abin da ake doruwa a kai, kamar misali, abin da muke dore a kai shine muna son tabbatar da addinin Musulunci ne. Ma’anar tabbatar da addini shine addinin Musulunci ya zama shi ke iko.
To, akwai abin da kuma ake ce masa ‘Policy’, shi kuma shine hanyar da za a bi a cimma wannan ginshikin –wato wannan manufar. To sai nace shi ‘principle’ baya canzawa, shi kuwa ‘policy’ yana iya canzawa. Nace alal misali, -na bada misali, bayan na yi bayanin ma’anar ‘principle da policy’ duk da yake kalmomin Ingilishi ne, sai nace alal misali, da yake a Zaria nake magana, sai nace idan za ka je Abuja, akwai hanya daga Zariya har zuwa Abuja idan ka yi kudu, kudu za ka yi ta yi hae ka je Abuja. To kana iya bin wasu hanyoyi, ko ka bi ta mota, ko ka bi ta jirgin kasa, ko ka bi ta jirgin sama.
Yana iya zuwa ya bi ta wata hanya ba wadannan da muka lissafa ba kuma, alal misali mai makon ya bi ta Kudu, sai ya bi ta Arewa, yace zai je Abuja ne, ya fada Hamadan sahara, sai ya fada Libiya, ya fada Baharur Rum, sannan ya gangara ya shiga Atlantic, ya zagayo ya shiga Lagos, ya wuce ya je Fatakwal, sannan ya hawo jirgi ya zo Abuja din, ko ya shiga mota. Ka ga dai ba gashi ya zo Abuja ba? Amma ya sha tafiyar da ta cika tsawo.
Tana iya yiwuwa kuma ya dauki hanyar ma da har abada ma ba zai iya zuwa Abujan ba, kamar ya bi gabas daga Zariya din nan, shine Yola, ya fada Kamaru, ya je shine Etopia, ya je har ya gama zagayensa ba zai taba zuwa Abujan ba.
Sai nace, saboda haka ‘policy’ kana bin ‘policy’ din da zai kai ka ga ‘gaya’ (inda ka nufa) ne. To, mu a shari’a muna da ka’ida. Kun san akwai abin da ake kira Machiavelli, sunan mutum ne, wani dan siyasa ne a Italiya aka yi shi ana ce masa Machiavelli, yana da ra’ayin cewa in ga abin da ake hankoro, to ba a damuwa in dai zai a cimma manufa ko ta wace hanya za a iya bi. Wato bai damu da ko ya halatta ko ya haramta ba, bashi da haram bashi da halas. Shine da Ingilishi yake cewa: “End justifies the means.” Ko da Arabiyya “Algaya tubarrirul wasila”, wato in dai za a cimma buri to ba za a damu da ta wace hanya aka bi ba.
To mu kuwa muna da shari’a. Shari’a ta nuna mana cewa in za a kai ga buri, to dole hanya din da za a bi ta dace da shari’a. Domin ba za ka aikata abin da ya haramta da nufin ka cimma burin abin da aka umurceka ka yi ba. Alal misali idan aka ce ka yi abu kaza wajibi ne, amma sai ka bi ta hanyar aikata haram wajen aikata shi ba. Wasu su kan ta kawo irin wannan a tunaninsu, wai sai su ce lalura ne, har su halattawa mutane aikata haram akan wai za a cimma wani buri. To muka ce mu ba a yin haka nan. Mu duk ‘policy’ dole ya zama bai sabawa shari’a ba.
To sai na ba da wani misali, misalin da na bayar, na san mutane har na kan ji tsoron basu misali, domin idan na ba da misali, wani baya tunanin Theory din, misalin kawai yake duba, kawai shikenan sai ya dauki misalin kawai. Har na kan ce to shikenan, a gane ainihin shi ‘theory’ din da na fada, ba misalin ba, amma misalai suna iya zama misalai da yawa.
Sai na ba da misali nace, ana iya kafa jam’iyyar siyasa. Sai nace to wannan ba ‘principle’ bane, ‘policy’ ne, ko da an yi jam’iyyar siyasa ba a canza ‘principle’ ba amma ‘policy’ ne, tana iya yiwuwa idan yanayi ya bayar cewa an aka da kuri’u, kuma a kidaya kuri’un, kuma wanda ya ci a bashi. –Wanda yake ba haka ake yi ba yanzu. Kuma mu ga cewa akwai maslaha wajen muma mu kafa jam’iyya ta tsaya takara, a ka da kuri’u ta ci zabe, mu ga cewa in haka nan zai yiwu mu ga cewa za a iya yi. Ko kuma a marawa wata jam’iyya baya saboda wani dalili, in misali aka ga wannan zai iya rage wani sharri ko kuma samun wani alkairi, alal misali.
Nace to amma wannan in aka yi mutane za su dauka ko an canza ‘principle’ ne, amma ba ‘principle’ aka canza ba ‘policy’ ne, saboda har ina cewa ita Harkar ba ita ce za ta zama jam’iyyar siyasa ba, ba fa zai yiwu ta zama jam’iyyar siyasa ba, ita addini ne, kuma ba za ta zama siyasa ba, amma tana iya samun jam’iyyar siyasa a karkashinta, ko ta marawa wata jam’iyya baya, amma tana nan a Harka Islamiyyah.
To sai na ba da ma misali, nace alal misali yana iya zama a babin maslaha, kamar a India, duk da yake suna da Musulmi sun kai kamar miliyan dari biyu –amma duk da haka su ‘minority’ ne. Kuma akwai irin masu tsattsauran ra’ayin Hindu din nan, wadanda suke adawa da Musulmi, to ya kan zama duk lokacin da aka yi zabe su dama ‘yan Hindun ne suka fi rinjaye, kuma dama su za su kafa gwamnati. To su kuma Musulmi suna neman wanne ne ya fi musu sauki a cikin wadannan. Akwai jam’iyyar da suke da zafin kishin addinin Hindu, ko sun hau basu ma Musulmi da kyau, to akwai kuma wadanda suma Hindu ne amma kuma suna da saukin kai ga Musulmi, saboda haka sai Musulmi suka ga gara su marawa wadanda suka fi sauki gare su.
Nace, kun ga ‘situation’ din India kenan. Na wani kasar yana iya zama daban, kowane zai lura da ‘situation’ din inda yake ciki ne. Bance muku wai nan ma (Nijeriya) sai ya zama haka nan ba, don nan ba India bane. An fahimta ai.
Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa.