Jaishi Shaheed Ahmad Zakzaky, Zainabiyyun, Ammar Bin Yaseeer Zone, Sun Gudanar da Taron Tunawa da Ranar Haihuwar Sayyada Zainabul Kubra (AS).

 


Jaish Shaheed Ahmad Zakzaky - Zainabiyyun, Ammar Bin Yaseer Zone, sun gudanar da taron tunawa da ranar haihuwan Sayyada Zainabul Kubra (As). Sun gudanar da taron ne na tsawon kwanaki biyu kamar yadda aka ayyana cikin jadawalin.


A Rana ta farko Alhamis 15 ga watan Disamba, 2022, da misalin ƙarfe 11:00 na Safe aka fara gudanar da taron, an fara ne da bude taro da Addu'a sai karatun Al-ƙur'ani mai girma, Sai aka karanta addu'o'i daban-daban ga ruhin su Shahidan musamman Zainabiyuun na rundunar Jaish Shaheed Ahmad Zakzaky, bayan kammala addu'o'in ne sai aka gudanar da wasanni daban-daban.


Ranar Juma'a 16 ga watan Disamba, 2022, itace rana ta biyu cikin jerin kwanakin da a gudanar da taron, inda aka fara da misalin karfe 4:00 na wannan Rana. Inda aka fara da bude taron da Addu'a sai wajabin maraba da baƙi, bayan wajabin maraba da baƙi ne Firqatu Shaheed Humaid (JAFSH) suka gabatar da display domin girmamawa ga ita Sayyada ɗin.


Malama Amina Sulaiman Bawa ta gabatar da wajabi bayan kammala display ɗin, tayi jawabi ne akan "Muhimmancin neman ili ga Sisters musamman Zainabiyyun". Tayi wajabi mai muhimmancin gaske tare da ƙarfafawa gasu Sisters ɗin, duk da yake jawabin na ta baya ta'allaƙa bane ga iya Sisters bane.


Bayan kammala wajibin nata ne wasu daga cikin Zainabiyyun na rundunar Jaish Shaheed Ahmad Zakzaky ɗin suka gudanar da faretin girmamawa ga ita Sayyada Zainabul Kubra(AS) tare da nuna farin cikin su da samuwar wannan Jaruma cikin Addinin Musulunci.


Bayan sun kammala ne aka yanka Al-kaki (Cake). Sai addu'ar rufe taron.


Daga ƙasa wasu ne daga cikin hotunan yadda taron ya gudana.


JASAZ Ammar Bin Yaseeer Zone

 17th December, 2022.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post