Jahilin Da Al'ummah Take Morar sa Yafi Me Ilimin Da Ba'a Morar Ilimin sa !!!


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]

imam ja'afar AL sadeeq alaihi Salam! 


Duk wani ruguntsumin dake cikin addini masu ilmi ne suke haddasa shi,  a yayin da ma'abota hankali suke zaune lafiya a cikin sa, 


Ban isa in kira ustazu yan tanshi da cewa Ba me ilmi bane,  in hakan ta faru to na yaudari kai na! Amma samun sa kuma cewa shi ma'abocin hankali ne, wannan Qullin yana buqatar bahasi! 


Lallai da ma'abocin hankali ne da ya iya banbance WANKAN TSARKI da WANKAN TSABTA! 


shi tambayar da ya amsa yake Jin cewa shima wani faqihi ne a duniyar ilmi (jurist) ita ce, 


SHIN SABULU NAJASA NE?

Wai da wannan tambayar ya rufe bakin malamai! Ya mance cewa Da zarar an yi magana sune a sahun Gaba wajen cewa lallai sai an komawa ga zantukan magabata! 


SHIN DUK CIKIN SU WAYE YA INGANTA SABULU CEWA YA INGANTA A YI WANKAN TSARKI DA SHI? 

Alagafarta malam, 

A cikin wankan tsarki sabulu najasa ne kuma abin Qi, domin shi Qazanta ne a cikin tsarkakakken ruwan da za'a yi wankan tsarki  da shi, kasancewar sa in har ya shiga ruwan to yana Gur6ata shi da ma'anar wankan tsarki!  duk abinda zai lalata Abu me tsarki kuwa to najasa ne,


Sabulu yana daga cikin sahun farko na abinda yake jirkita ruwan tsarki shi kuma wankan tsarki malamai bisa IJMA'I sun ce shine wanda yake dauke warin da jiki yake yi wanda ake samu musamman lokacin jima'i ko kuma Biqi da haila ko Don tsabtace jiki domin shiga musulunci ko wankan idaini da juma'at,, saboda wankan guda biyu ne shi yasa malamai suka ce manzon Allah sallallahu alaihi wa Aleh wasallam ya ce bayan Ka yi na tsarki babu lefi kuma Ka dora na sabulu, Mu masu hankali mun San cewa a I a lokacin a kwai sabulu amma aka raba wankan ya zama biyu ko wanne da sharadin sa,  Me ilmi Irin su ustaz sun kasa gane abinda yake ta6a spiritual, wato (RUH) da kuma body (JASAD)  wankan tsarki ba jiki yake wankewa ba,  Don haka baka buqatar sabulu alagafarta malam, 


Magabata suka tura suka ce me wankan Sabulu wanda baya yin Irin wancan wankan na tsarki yake yin na sabulu, (tsabta) Shine ake Jin Irin warin da wancan wankan tsarkin yake cirewa a jikin sa!  


Wato malamai Irin su dutsen tanshi, su suna iya yin ijtihadi sannan su Qaurace wa zantukan magabata kuma su zauna lafiya har ma a dinga ganin cewa sun fitar da wani ilmi wanda a baya babu shi,  a yayin da wasu malamai da basa layin fahimtar addini Irin ta su dutsen tanshi in suka aikata hakan hukuncin su shine duka da dauri, a baya malam Ibrahim khalil da Irin wannan tunanin yayi amfani wajen bada fatawar halaccin yin alwala ko tsarki da lemon kunun zaqi ko kuma na coca cola, duk da ko Sau daya malamin bai ta6a gwadawa a gaban almajiran sa ba! 

tabbas sabulu ba najasa bane amma a inda aka hana amfani da shi a al'amarin addini Ka yi amfani da shi ya zama najasa! Tunda dai kasan sharadin ingancin ruwan wankan tsarki da abubuwan da ba'a son su a ciki!


Nima da hankali na yi magana Don bani da ilmi!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post