Jagorancin Gado Da Siyasar Maslaha Da Rashin Cancanta!!!

 



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 




Dole a samu babbar matsala indai ya zama gado da siyasa su suke naɗa Jagorancin Addini ba cancanta ba tun a matakin farko .

Mafi yawancin matsaloli ko rashin dacewa da ake gani daga wasu jagori na ɓangarorin Addini ya samo asali ne daga rashin cancantarsu da jagorancin tun ran gini , ko kuma kallon wasu maslahohi na Duniya tsantsa ba wai dacewar su da hakan bisa ingantaccen ma'auni . Rarrabe wannan zance kuwa shine kamar haka :


Za ka sami wani babban Shehi ko Malami yana da tarin mabiya da almajirai wanda ba gadar su yayi a wajen kowa ba , kawai dai zaɓi ne na Allah da cancantar sa suka saka ya zama haka , amma da zarar ya rasu sai aga al'amarin Makarantar sa, Gidansa da gudanar da mabiyansa ya taɓarbare , me ya jawo hakan ? Shine damƙa su a hannun da bai cancanta a damƙa su ba , kawai dai an samu wani daga cikin ƴaƴan sa aka damƙa masa ragamar nan ba tare da an duba dacewa ba , kawai dan dai yana ɗansa ne .


Bance ɗa ya gaji uba aibu bane abune mai matuƙar kyan gaske , Hausawa na cewa kyan ɗa ya gaji uban sa, sai dai ina cewa in ya zama ɗan ya cancanci ya gaji uban ta dukkan fuskokin cancanta shine abun zai kyau , ko ma so samu yafi Mahaifin nasa ilmi ko wasu ɓangarorin nagarta da mahaifin bai mallake su ba , dama cika ta Allah ce .

Amma in ba haka ba ! Wani Ɗan zalunci ne da babban aibu ace shine ya gaji mahaifinsa , domin baya zama sanadiyyar ci gaba da ɗorawa daga inda mahaifin ya tsaya , sai dai ma ya rusa ƙoƙarin mahaifin da ya ƙarar da shekarun sa yana yi .


To daga sanda aka samu irin wannan nau'in magaji shikkenan sai harkar jagoranci da gudanarwa su shiga wani Wadi , ayi ta samun rikici da rarrabuwa a tsakanin mabiya ko ma daga ƙarshe komai ya lalace .


Wannan ta fuskar gado kenan , haka ta fuskar Jagorancin da ake naɗawa ba tare da an duba cancanta da dacewa ba , sai dan maslaha da kallon abun Duniya aka naɗa shi . Bance kwarai-kwata kallon maslahohi bai da amfani ba a anan , musamman ma da ya zama jagoranci ne na siyasar gudanarwa ne ba wai jagoranci bane na haƙiƙa .

Daga nan ne kuma za mu fahimci uwa uba ko kuma jigon da yake jawo waɗannan matsalalolin shine : yadda aka ɗauki Jagorancin Addini da Tafyai ta Allah a matsayin siyasar Duniya da Maslaha kawai , Siyasar da Siyasar da bata Addini ba sam , memakon a dogara da ma'aunai na Addini da cancanta bisa zaɓin Allah Ta'ala.


Shi yasa Mu (Shi'a) muke ƙara godewa Allah Ta'ala a irin waɗannan Mas'alar , bisa ni'ima da luɗfin "Marja'iyya" da yayi mana a wannan zamani na Babbar Fakuwar Ma'abocin Zamani (Alghaibatul Kubra) da muke ciki .

Domin kuwa Marja'iyya ta zama wata garkuwa da ta ije mana faɗawa irin wannan hauma-haumar ta Jagorancin gado da kuma siyasar Maslahar ba tare da duba cancanta ko dacewa ba .


Allah ya tsare mana shigar Gadon Nasaba da Siyasar Maslaha cikin al'amarin Marja'iyya, ba komai bane yake tasiri a wannan fagen face Taufiqi da tsantsan luɗufin Ubangiji , amma ba dabara , ilmi ko dukiyar mutum ke bashi hidimar Almarja'iyyatul Ulya ba , tun daga zamanin wakilcin Ai'mmatu Ahlil baiti (a.s.) da zamanin Jakadanci tun ƙarni na uku har zuwa yau a haka ake , Alhamdulillahi. Nadan wani zai ce : Uhm anan .


Wata ƙila wannan ya samo asali ko yana da alaƙa da tushe ko tubalin da Aƙidar Shi'a Imamiyya ta ginu akai , cewa Imamanci da Khalifanci sha'ani ne na zaɓin Allah da Nassin Ma'asumi kafin da bayan Ma'asumi, Manzon Allah (saww) Imami ne da zaɓin Allah , haka nan Imam Ali da sauran Ai'mmatu Ahlil baiti (a.s.) goma sha ɗaya ba iya gado bane ya basu Imamanci da Khilafa , ba wai dan kawai suna zuriyar Annabi bane suka zama hakan domin akwai wasu zuriyar Annabin bayan su kuma ba Imamai bane . Kenan zaɓin Allah , cancanta , dacewa da falalar Ubangiji ce ta basu wannan matakin ba siyasar maslaha da ra'ayin wasu mutane bane .


To da ace ana alaƙanta jagorancin Addini da barwa zaɓin Allah da cancanta da ba'a afkawa dayawan matsalalolin da ake fama da su ba , dama yadda ake ganin sakin layi ko wuce gona da iri da wasu jagorori ke yi , ko da yake Hausawa sukan ce : Tun ran gini tun ran zane .


Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post