Insha Allah a munasabar Maulidin Sayyada Zahra Salamullahi Alaiha dake gabatowa na da wasu kwanaki, zamu bada jarin kasuwanci ga mata 5 wadanda suke da 'Business model canvas' da zasu iya farawa da ₦20,000. !!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 

Ga waɗanda suke da Business Plan din su a ƙasa, zasu iya turo wa kai tsaye ta hanyar email address sambaaliyu@yahoo.com


Za mu tantance mu zaɓi 5 daga cikin su insha Allah da zamu fara bawa jarin ₦20,000. Wannan shirin ya taƙaita ne ga mata zalla dake arewacin Najeriya musamman masu wala'i da Ahlul Baiti. 


An bude damar turo da 'Business Model Canvas' daga yau har zuwa 1 ga watan Janairun shekara ta 2023.


Kada a manta da sanya sunan da ake amfani da shi a kafar sada zumunta ta facebook.


Allah ya ƙara tsira da aminci ga shugabar mu Nana Fatimatuz Zahra.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post