Ina lillah wa Inana Ilaihi Raji'uun!!!




Allah ya yiwa mai Martaba Ayatullahil Uzma Sayyid Muhammad Saadiq Al-Rouhani Rasuwa a yau Juma'a 21ga watan Jumadhal Ula 1444H , ya rasu yana da Shekara 96 a duniya .


Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin Maraji'an da suka yi karatu a birnin Najaf mai Alfarma, kuma ɗaya daga cikin Maraji'an Taqlidi dake zaune a birnin Qum-Iran . Ya ƙarar da rayuwarsa cikin yiwa Addini hidima ta hanyar karatuka da rubuce-rubuce masu yawa , daga cikin Littattafansa akwai Littafin "Fiqhus Sadiq " 


Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin manyan Almajiran Jagoran makarantar Hauza Ilmiyya, wato Ayatullahi Sayyid Abul-Qasimul Khoei (Rahimahullah) , kuma ya samu Shedar Ijtihadi daga Sayyid Khu'i yana ɗan shekara sha hudu a duniya .


Ya zo a ruwaya cewa : Idan Malami ya rasu an samu wani giɓi a Musulunci da zai ba taɓa cikuwa ba har ranar Alƙiyama .


Allah yayi masa Rahama da Gafara ya tashe shi tare da Annabi da iyalan gidansa tsarkaka.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post