In Ka Fahimci Al'amarinsu Tashi Za Kai Ka Nemi Iliminsu .....!

 





[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 




In har Allah ya maka gam da katar ka fahimci tafiyar Ahlul Baiti (a.s.) wajibi ne ka tashi ka nemi ilmin Ahlul Baiti (a.s) iyakar yinka , tun daga matakin Aƙida , Fiqhu da Suluki . 

Ba wai zama za kai ka naɗe hannu da ƙafa kace kai yanzu ka fahimci gaskiya kowa ba akan daidai yake ba , a'a ! Dole ka tashi ka nemi Ilmin da yake tabbatar da ingancin gaskiyar da ka fahimta , ko da kuwa kai Malami ne a ƙungiya ko Mazhabar da ka bari .


Dan kana Malami a ƙungiya ko Mazhabar da ka bari , hakan baya nufin ka zama malami a Shi'ar da ka fahimta , bari ma dai daga lokacin za ka fuskanci wani ƙalubalen da wata ƙila yafi wanda ka tsallake a baya , shine Ƙalu balen neman ilmin sanin Ingantaccen Shi'anci .

Amma idan ka dogara da cewa kai Malami ne kafin ka fahimci Shi'a dan haka yanzu ka zama malamin Shi'a to ka yaudari kanka , kuma in baka yi da gaske ba sai ka jawowa kanka abinda ake cewa ɓata bayan shiriya , Kuma hakan zai iya kaika ga ka dinga cutar da tafiyar fiye da wanda shi bai ma yarda da ita ba balle ya bita, tunda shi yana daga waje yake kawowa tafiyar hari da ƙokarin cutar da ita , kai kuma kana daga cikin za ka dinga wasu abubuwa da sun saɓawa tafiyar gaba ɗaya , za kai ta ɗebo tun tunani da abubuwan tafiyar da kabari kana ta guringunɗuma da su, ko ka zama silar Saddu ga wasu da basu fahimci tafiyar ba .


Maganar gaskiya Shi'anci ba kamar ko wacce tafiya yake ba ta fuskar tsari , akwai Jagoranci da Marja'iyya a Shi'anci ba sakaka al'amuran suke ba tun a zamanin rayuwar Ai'mmatu Ahlil baiti (a.s.) da lokacin Alghaibatul Kubra da muke ciki yanzu.


Ma'anar ka fahimci al'amarin Ahlul baiti (a.s) shine : Yanzu ka yarda da cancanta da jagorancinsu a bayan Manzon Allah (a s.) , Kuma yanzu sune makomar da za ta ja ragamar Addini da rayuwarka ta hanyar ƙudurcewa da aikata duk wani abu da ya tabbata daga garesu har ma wanda bai riskeka ba na daga umarni da hani ko Irshadi.

Amma meye amfanin kace ka fahimci al'amarin Ahlul baiti (a.s.) kuma Aƙidarka , Ibadarka da komai na rayuwarka ya sabawa karantarwarsu ka sani ko baka sani ba ? Meye amfanin fahimtar da kai baka bita ba ?

Imam Ja'afar Assadiq (a.s.) yana cewa ; Naso ace na daki Almajiraina dan su fahimci Addininsu .

 

Maganar gaskiya indai da gaske ka fahimci Ahlul Baitin ka tashi ka nemi Ilminsu , ka ajiye wani malamanta (akwai wanda sun shafeka a wannan fagen ) , ka ajiye batun jagoranci da nine wane a da can kabi bi na sosai , ka nemi ilminsu a wajen waɗanda Allah ya fuwacewa ko kaima ka samu rabauta .


Haka nan in ma ba Malami bane kai ka fahimci tafiyar ne dai ko ta wace hanya , to dai dole ka ka tashi ka nemi ilmi da sani , domin ilmin shine ginshiƙin tafiyar da tsira Duniya da Lahira .

Kar ka yarda ka ruɗi kanka da kowanne irin abu ka zauna ka ƙi neman Ilmi , ko ba komai neman ilmin Farilla ne akan dukkan Musulmi, kuma kai kanka ba zaka ji daɗi kayi alfahari ba in baka nemi ilmin su ba , domin sanin ilmin nasu ne zai sa ka ƙara fahimtar ni'imar da Allah yayi maka , ta yanda zaka iya ƙiyasta inda ka baro da inda kake dan ka fahimci akwai banbancin da gaske .Tabbas in kabi ruɗu za ka ga ruɗu , kuma wannan doka ce gamammiyya da hankali ke iya riskarta cikin sauƙi , duk a tafiya , ɓangare ko fannin da kake kana buƙatar sanin ilminsa kafin ka zamo Ahlinsa , ba za kuma ka samu ilmin ba sai ka zauna da Ahlinsa da waɗanda suka keɓanci da wannan bangaren .


فَتَعَالَى اللَّهُ الْمَلِكُ الْحَقُّ ۗ وَلَا تَعْجَلْ بِالْقُرْآنِ مِن قَبْلِ أَن يُقْضَىٰ إِلَيْكَ وَحْيُهُ ۖ وَقُل رَّبِّ زِدْنِي عِلْمًا ......


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 


1/Jumadha Thani/1444H -25/13/2022

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post