[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Daga cikin Shubhohin da suke bijiro mana dasu sukan ce : Indai da gaske an kwace Fadak daga Sayyida Zahra (a.s.) bayan Shahadar Annabi (a.s) , me yasa da Mijinta Ali bin Abi Ɗalib (a.s.) ya karɓi ragamar Gwananti bai dawo da ita ba ?
AMSA :
1 . Kowa yasan cewa Shekaru kusan 25 sun shuɗe mafi yawancin Musulmi an ruɗesu da cewa Fadak na daga Dukiyar Gwamanti , kuma wani ɓangare ce na Baitul Mali dole ayi amfani dasu ga Maslahohin Musulmi baki ɗaya , Saboda Gwamnatoci Uku da suka gabaci Imami sun sa mutane sun tafi akan hakan , Tom in Imam Ali (a.s) ya ɗauki Fadak ya bayar da ita ga Imam Hassan da Hussaini (a.s.) misali , mutane za su tuhumeshi da ɗibar dukiyar Gwamnati kamar yanda Usman yayi ga makusantansa .
Duk da akwai ƴan kaɗan daga Sahabbai da sun san haƙiƙanin gaskiya amma mafi yawan mutane a lokacin sun jahilci gaskiya.
Kuma a lokacin ya kasance yana kashe abunda ake samu daga Fadak ga Maslahar Musulmi da Musluunci dan haka babu wani babanci koma kamar ya karɓa din ne .
2 . Kasancewarsa Khalifa na Shari'a kaɗai ya wadatar da tabbatar da ita (FADAK) tamkar tana hannunsa ne , Sawa'un ya maida ita hannunsa (a Keɓance) ko bai mayar ba ya barta a hannun Gwamanti (a Game) duk dai a ƙarshinsa take , shi yasa ya faɗa a wata Huɗuba a cikin Nahjul Balagha yace Fadak ta Faɗima (a.s.) kuma yanzu tana hannunsa , Lokacin da ya rubuta Wasiƙa zuwa ga Usmanu Bin Hunaif a Basra yake cewa :
بلى كانت في أيدينا فدك من كل ما أظلته السماءُ، فشحت عليها نفوس قوم، وسخت عنها نفوس آخرين، ونعم الحكم الله.
3 . Da ace Imam Ali (a.s) yana karbar Gwananti ya dawo da Fadak ga Ƴaƴansa , da Maƙiyansa za su tuhumeshi da son Duniya suce yana hawa ma ya ɗibi Dukiyar Gwamanti ya bawa zuriyarsa Dukiyoyi , amma hakan da yayi ya tabbatar musu da cewa shi ba Duniyarsu bace a gabansa , tun farko sun nemi haƙƙinsu ne saboda ita ma'aunin ce Shari'a da za'a gane Halastaccen Khalifa da akasinsa , duk da a hakan ma irinsu Ibnu Taimiyya sai da suka Siffanta Sayyida Faɗima (a.s.) da kwaɗayi da son Duniya .
4. Uwa uba akwai ruwayoyi da aka ruwaito daga Ahlul Baiti (a.s ) da suke faɗar Illa da kuma Hikimar data sa Imam Ali (a.s) bai dawo da Fadak ba , daga ciki akwai riwayar data Nassanta cewa :
Da waɗanɗa suka yi ƙwacen da wacce aka yiwa kwacen duk sun koma ga Allah Ta'ala, Allah yayi Uƙuba ga wanda yayi ƙwace sannan ya sakawa wacce aka ƙwacewa da Lada , sai Imam ya Ƙyamaci ya dawo da abinda Allah ya riga yayi hukunci na Adalci akansa . Kamar yanda Sheik Assaduuq (Rahimahallah) Ya Rawaito a cikin Ilalus Sharaa'i'i Juzu'i na 1 , Shafi na 154 , Babi na 124 yace :
العلة التي من أجلها ترك أمير المؤمنين (عليه السلام) فدكا لمّا ولي الناس : بإسناده إلى أبي بصير عن الإمام الصادق (عليه السلام) ، قال : « قلت له : لمَ لمْ يأخذ أمير المؤمنين (عليه السلام) فدك لمّا ولي الناس ، ولأي علة تركها ؟ فقال : لأن الظالم والمظلومة قد كانا قدما على الله عز وجل ، وأثاب الله المظلومة وعاقب الظالم ، فكره أن يسترجع شيئاً قد عاقب الله عليه غاصبه وأثاب عليه المغصوبة» .
5 . Wata riwayar kuma tace koyi da Manzon Allah (saww) yasashi yin hakan, domin lokacin da Manzon Allah (Saww) yayi Hijira Aƙilu ɗan Abi Ɗalib ya siyar da gidansa , da aka tambayi Annabi bayan Fathu Makka me yasa bai dawo dashi ba ? Sai yace : Mu wasu iyalan gida ne da bama dawo da abinda aka ɗaukar mana da zalunci . To dan haka ne shima Imam Ali (a.s) bai dawo da Fadak ba . Duba Ilal na Sheik Assaduuq a lambar data gabata za kaga yana cewa :
عن إبراهيم الكرخي قال : « سألت أبا عبد الله (عليه السلام) فقلت له : لأي علة ترك أمير المؤمنين فدكا لمّا ولي الناس ؟ فقال : للاقتداء برسول الله ( صلى الله عليه وآله ) لمّا فتح مكة ، وقد باع عقيل بن أبي طالب داره ، فقيل له : يا رسول الله ألا ترجع إلى دارك ؟ فقال ( صلى الله عليه وآله ) وهل ترك عقيل لنا داراً ، إنا أهل بيت لا نسترجع شيئاً يؤخذ منّا ظلماً ، فلذلك لم يسترجع فدكاً لمّا ولي» .
6 . Ruwaya ta uku ta bayyana cewa Imam Ali (a.s) ya kasance Adalin Jagora mai yaɗa Adalci da kawar da zalunci , mai ƙwatowa waɗanda aka Zalunta haƙƙinsu , Majiɓincin lamarin Muminai da yake kare haƙƙinsu , kuma ya san shi Allah ne kaɗai me ƙwato masa haƙƙinsa ya taimakeshi akan Azzalumai , kamar yanda Sheik Assaduuq ya Rawaito a Babin da ya gabata cikin Ruwaya ta uku yace :
عن علي بن الحسن بن فضّال عن أبيه عن الإمام الكاظم (عليه السلام) قال : « سألته عن أمير المؤمنين (عليه السلام) لمَ لمْ يسترجع فدكاً لمّا ولي الناس ؟ فقال : لأنّا أهل بيت لا نأخذ حقوقنا ممّن ظلمنا إلا هو ( يعني إلا الله ) ، ونحن أولياء المؤمنين ، إنما نحكم لهم ، ونأخذ حقوقهم ممّن ظلمهم ، ولا نأخذ لأنفسنا» .
Waɗannan dalilai sune sababai da hikimomin da suka sa Imam Ali (a.s) bai sake dawo da Fadak ba a lokacin da ya karɓi ragamar Gwamanti (a.s.) .
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
5/Jumadha Thani/1444H- 29/12/2022 .