Idan har Annabi Muhammad (saw) Zai Yi koyi da Yahudawa wajen yin Azumin Ashura; to me Zai Hana Musulmai koyi da Kiristoci wajen yin bikin Kirsimeti???

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 

Bukin Kirismiti.

2. Idan Annabi Muhammad(saw) Yace a Azumci Ashura don Musulmai sun fi kusanci da Annabi Musa(as) akan Yahudawa; kenan Musulmai ya kamata Su yi bikin Kirsimeti don sun fi kusanci da Annabi Isa(as) akan Kiristoci???

3. Shin akwai wata ayar Qur'ani ko ingantaccen hadisi da karara ya hana Musulmai taya Kiristoci murnar bikin Kirsimeti???

4. Su waye Ahlul-Kitabin da Qur'ani ya halatta mana kyautata masu?

5. Su waye Ahlul-Kitabin da Qur'ani ya halatta mana aurensu?

6. Su waye Ahlul-Kitabin da Qur'ani ya hallata mana cin abincinsu?

7. Annabi Muhammad(saw) ne ya kirkiro Siyasar Dimukuradiyya? 

8. Wane Sahabi ne ya taba kafa fatin jam'iyya?

9. Idan duk abinda ya samo asali daga Kiristoci da Yahudawa haramun ne; kenan Siyasar Dimukuradiyya ma haramun ce?

10. Kenan haramun ne Musulmi yayi tarayya da Kiristoci da Yahudawa wajen yin zabe ko a zabe shi a tsarin Dimukradiyya?

11. (a) Ina Shaikh Abubakar Gumi ya samo hujjar fifita Dimukuradiyya akan Sallah?

(b) Taya abinda Kiristoci da Yahudawa suka kirkiro ya fi Sallah?

12. (a) Ko kun san Kirista ne ya Jagoranci sake fasalin Masallacin Abuja (The Abuja National Mosque)?

(b) Me ya sa lokacin da za'a yi gidauniyyar sake gina Masallacin aka bari Obasanjo ya jagoranci aikin awancan lokacin?

(c) Idan bai hallata Musulmi su yi tarayya da Kiristoci ba; kenan ya Zaba wajibi Musulman da suka yi Sallah a gurin su ranka, sannan a daina Sallah a Masallacin ko a cire fasalin da Obasanjo ya sa aka yi?

13. (a) Shin Sahabbai sun ci abincin Kiristocin Habasha ko nasu suke dafawa a lokacin suka yi Hijira zuwa Habasha?

(b) Idan haramun ne Musulmai suyi huld'a da Kiristoci; to me ya sa Annabi Muhammad(saw) ya tura Sahabbai Hijira zuwa Kasar Kiristocin Habasha?

14. Idan dukkan Kiristoci mushirikai (babu nagari cikinsu); me ya sa Qur'ani zai halatta mana aure, cin abinci da kyautata masu?

15. Idan Annabi Isa(as) na Banu Isra'ila ne kawai; me ya sa Qur'ani zai hana Musulmai nuna bambanci tsakanin dukkan Annabawan Allah(saw)?

16. (a) Idan akwai shakku da rashin tabbas akan cewa ba lalle ne 25 ga watan Disamba aka haifi Annabi Isa(as); to akwai tabbacin cewa ranar Ashura Allah ya tseratar da Annabi Musa(as) daga Fir'auna?

(b) Idan za'a iya haramta bikin Kirismiti,

Mai zaihana Kuyi juyayi Kashe Jikan Manzon Allah(h) Imam Hussain (as)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post