Idan Duk Hadisin Da Ke Cikin Sahihul Bukhari Ingantatttu Ne......!!!


@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@


Hadisi na 4240 da na 4241, ruwaya daga Uwar Muminai Nana A’isha matar Annabi (S), tace: Fatima ‘yar Annabi (SA) ta aikawa Abubakar da sako tana mai tambayarsa a kan abin da ta gada daga Manzon Allah (S) na daga abin da Allah ya bashi a Madina da Fadak, da kuma abin da ya yi saura daga Kumusin Khaibar. Sai Abubakar yace mata; Ai Manzon Allah (S) yace: ‘Ba a gadonmu! Abin da muka bari sadaka ne… Sai Abubakar ya ki ya ba Fatima komai. Sai Fatima ta yi sabani da Abubakar a kan wannan, (cewarsa babanta yace ba a gadonshi), sai ta ƙaurace masa, har ta yi wafati bata sake masa magana ba. Kuma ta rayu ne bayan wafatin babanta da watanni shida. A yayin da ta yi wafati, mijinta Ali ne ya birne ta a cikin dare. Ba a gabatar da Abubakar gareta ba kuma bai sallaci gawarta ba.”


Haka ma a Hadisi na 6726 a Sahihul Bukharin, aka ce bayan da ta nema, Halifan ya ce mata Manzon Allah (S) yace ba a gadonsu su Annabawa. Sai Sayyida Fatima (S) ta ƙauracewa Abubakar, ba ta sake masa magana ba har ta koma ga Allah (T).


Duk wadannan kila kace gaba ɗaya hadisan guda uku da na kawo ba a ce ta yi fushi da shi ba, an ce ta kaurace masa ne. Sai Imamu Bukhari yace idan ka kasa bambance ma’anar kauracewa mutum da kuma yin fushi da mutum, ka koma baya zuwa ga Hadisi na 3093, an kawo cewa, da Abubakar yace wa Fatima (SA), ai Manzon Allah (S) yace; “Ba a gadonmu, duk abin da muka bari sadaka ne.” Sai Fatima ‘yar Manzon Allah (S) ta yi fushi, ta kaurace ma Abubakar. Bata gushe ba tana mai kaurace masa har ta yi wafati. Kuma ta rayu ne bayan wafatin mahaifinta da watanni shida.


Muka ce, a matsayin Sayyida Fatima (SA) na 'ya ɗaya tilo da Annabi (S) ya yi Wafati ya bari, shin Manzon Rahma (S) da ya zo mana da ayar Wasiyya, ya fada mana falsafar wasiyyar, ya ma wannan 'yar tasa tilo Wasicci kebantacciya zuwa gare ta a kan ba a gadonsa shi, tunda ya riga ya fadawa duk al'ummar Musulmi cewa duk Musulmi na gadon mahaifinsa?


Malam Buhari yace sirri guda Annabi (S) ya yi da 'yarsa a yayin jinyarsa. Ya bamu labarin a Hadisi na 3715 da na 3716 a cikin Sahihin Bukhari; A’isha matar Manzon Allah (S) tace, Annabi (S) ya kira ‘yarsa Fatima (SA) a lokacin rashin lafiyar da ya yi wafati a cikinta. Sai ya yi magana (cikin sirri) da ita, sai ta yi kuka. Sai ya kuma kiranta ya yi sirri da ita, sai ta yi dariya.’

 

Nana A’ishatu ta cigaba da cewa: Sai na tambaye ta akan wannan sirrikan da ya mata (Bayan wafatin Annabi (S). Sai tace min, “Annabi (S) ya sirranta min cewa zai yi wafati a cikin wannan rashin lafiyar da ya yi wafati a cikinsa. Sai na yi kuka. Sai ya kara sirranta min cewa ni ce farkon wacce zan bi shi a cikin iyalan gidansa. Sai na yi dariya.”


Imamu Bukhari da raba aiki, sai kuma a Hadisi na 3714 a cikin Sahihul Bukhari, ya ruwaito mana cewa Manzon Allah (S) yace: “FATIMA TSOKAR JIKINA CE, DUK WANDA YA FUSATA TA, NI YA FUSATA.”


Ya Salam!!! Gaba daya Imamu Bukhari ya ruɗani wallahi. Kace Sayyida Fatima ta yi fushi da Sahabi, kuma ka kawo mana cewa Annabi yace fushinta fushinsa ne. Mun kuma sani sarai cewa fushin Annabi fushin Allah Ta'ala ne. Allah Ya sa ba nufin Imamu zagin Sahabbai bane, domin mawakinmu na Sunnah yana cewa: "Sahabbai Yan Gatan Allah."


Mu yi salati, Hadiyya zuwa ga Abar Zalunta; Sayyida Zahra (SA). ❤️

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post