Idan bamu yi da gaske ba tabbas za a bar mu a baya. (Daure ka karanta duka)!!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]

A daidai lokacin da duniya ke samar da sababbin tsare tsare da cigaba a fannin fasaha, mu anan har yanzu ana tare da tsohon tsari a kusan duk fannonin da an riga an wuce inda muke a duniya. 


Ina fargabar nan da wasu yan shekaru masu zuwa, kaso mai yawa na mutane a fannoni daban daban zasu rasa aikin yi, sakamakon an samar da wata fasaha ta 'Artifitial Intelligence (AI)' da zata yi kusan komai ba tare da an samu tangarɗa ba. 


Mu fara da ɓangaren aikin jarida, da yawan yan jarida suna nan sun takaita kansu a yawon taron manema labarai da wallafawa, karantawa, fassarawa ko tattara rahotanni, wanda a yanzu da nake magana akwai manhajoji da akai na (AI) da zasuyi kusan duk wadannan, kuma wasu kamfanonin labarai sun fara samun ilimi akan su har ma sun sallami ma'aikata da yawa. Duk wani labari yanzu ta wannan salo na fasaha suke tattara shi, su hada shi, su wallafa, sannan ma su fassara shi ba tare da samun tsaiko ko kusakurai ba. 


Mu dawo bangaren marubuta labari wanda ake tattarawa a mai da shi shirin wasan kwaikwayo da sauransu, cikin sakanni da basu wuce 10 zuwa 20 ba, akwai manhajoji da za su rubuta maka labarai kala kala a tsari na 'Script' wanda kawai aikin 'shooting' ne ya rage. 


Mu koma kan masu zane, akwai manhajar (AI) da kawai gaya mata abinda zata zana maka zakayi, zata zana shi cikin sakanni 5 zuwa 10. 


Mu koma kan masu aikin tace hoto 'Video Editing', akwai manhajoji na AI masu tarin yawa da zasu gyara maka bidiyo su tace shi su fitar maka, kai har ma da wanda zasu iya wallafa maka su kai tsaye a dukkan shafukan ka na sada zumunta da YouTube kana daga zaune cikin kankanin lokaci. 


Hatta wannan rubutu da nayi, akwai manhajar da zata iya mayar mun da shi bidiyo da sautin murya, har ma da wadda zata iya sanya wa a ganni ina bayanin duk abinda ke rubuce anan ba tare da na zauna gaban Camera ba, ba tare da nace uffan ba, har muryata zata yi da motsawar lebe na a sanda take bayani. Kaji Abu uwa tsafi ko?


Akwai manhajar AI da zata rubuta maka kowacce irin maƙala kake so cikin duk wani yare da kake so, abin mamakin shine za ka samu maƙalar cikin sakanni kasa da 10. 


Akwai manhajar da aikin ta shine idan an ɗauki sauti, zata cire hayaniya da shiru da kuma duk abinda zai lalata kyan sautin duka shima cikin yan sakanni kadan. 


Akwai manhajar AI da kawa labari zaka rubuta, ita kuma zata nema maka 'Headline' sama da 10, sai ka zabi wanda yayi maka. Akwai ma wadda zata sake maka irin wannan labarin sak, kawai abinda zata sauya shine kalmomin. 


Kai akwai manhajar da zata dakatar da aikin editoci a jarida, don cikin dan lokaci zata gyara kusakurai na Turanci da na grammar ta tace maka rubutun ka tsaf, kawai wallafa kake jira. 


Idan zan cigaba da zayyano su, kai kan ka zaka gaji. Akwai wadda duk tsayin rubutu kawai ka dora Mata zatayi maka abinda ake cewa ''summary'', cikin yaran jumloli zaka fahimci duk abinda ke cikin wannan dogon rubutu da akai. 


Anya kuwa ba za a barmu a baya ba duba da cewa wadannan manhajoji ba wai kwanan nan suka fito ba, amma mafi yawan mutane basu san su ba harma da wadanda suke cikin tsarin da ta dace su sani. Dole yan jarida da sauran marubuta sun tashi tsaye don tafiya daidai da zamani, su zo da abinda wadannan manhajojin basa yi domin nan kusa da yawa zasu rasa aikin yi, da wannan sababbain tsare tsare za a koma gudanar da mafi yawan ayyuka. 


NB: Hatta wannan hoto dake kasa manhajar AI ce ta samar dashi, kawai ce mata nayi "A young boy sitting on the street with his phone and a laptop''. Rubutun kuma daga alƙalamin Aliyu Samba. 


©Aliyu Samba

21/12/22

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post