Lukman Tukur Ty
Hukuncin kisa kan jagoran darikar qadiriya riduljannah kuma shugaban as'habul khafi warrakim wato Ash Sheikh Dr Abduljabbar nasiru kabara,
Ba saboda batanci ga Annabi S A W bane siyasa ce kawai da kuma tsama dake tsakanin sa da wasu malaman jahar Kano da kuma gomnatin jahar Kano,
Dan kuwa kotu'nan Nigeria kam babu wata kotun da zata iya yankewa wanda yayiwa Annabi S A W hukuncin kisa babu ta balle kotunan jahar Kano.
Misali: A shekarun baya wani matashi mai suna Mubarak bala mai shekaru da basu gaza 37 ko 40 ko 40+ ba.
Yayi mummunan batanci ga Annabi S A W tare da wasu laifuka sha 17 idan kahada da batanci ga Annabi S A W sun zama sha 18.
A take hukumar yan sanda wato police takamashi inda ta gama hada hunjojinta akan sa ta kaishi kotu bayan ankwashe tsawon lokuta ana fafata shari'ar ,
Daga bisani Mubarak bala ya jaddadawa kotu ya aikata laifin da ake tuhumar sa dashi na yin batanci ga Annabi S A W tare da saura laifuka sha 17, yazama sha 18.
Inda take kotu ta yanke masa shekaru 45 a gidan kaso, abin mamaki 🤔 wanda yayiwa Annabi S A W batanci ace iya shekaru 45 aka yanke masa,
To bama shine abin daure kai ba dan kuwa su wadan nan shekaru 45 da aka yankewa Mubarak bala bawai iya na batanci ga Annabi S A W bane kadai a a,
Anyankewa Mubarak bala hukuncin shekaru 45 ne bisa laifuka sha 18 ci harda batanci ga Annabi S A W idan alkali mai shari'a ya yanke hukuncin ne bisa ko wane laifin hukuncin sa shekaru biyu da yan watanni ciki harda batanci ga Annabi S A W.
Kamar yadda zakuji a wannan rahoton shari'ar ta sa,
dan haka batanci da Mubarak bala yayiwa Annabi S A W Shekaru biyu da yan watanni ne aka yanke masa
To taya har kake murna akan hukuncin zalunci da aka yankewa Sheikh Dr Abduljabbar nasiru kabara da sunan batanci ga Annabi S A W bayan masu batanci ba'a iya hukuntasu.
Munane mudawo hayyacin mu wlh...