Hukuncin Da Kotun Kano ta yanke akan Shaikh Abdulja bar kabara,

 





Babbar kotun shari'ar Muslunci dake zaman ta a Kofar Kudu ƙarƙashin Mai Shari'a Alkali Ibrahim Sarki Yola ta yankewa Sheikh Abduljabbar Kabara hukuncin hukuncin kisa ta hanyar rataya dogaro da sashe na 392(b) na Kano state Shari'a Penal Code. 


Kotun ta yanke hukuncin ne bayan bayyana ra'ayin ta game da shari'ar da aka ɗauki tsawon shekara da watanni ana gudanarwa a babbar kotun shari'ar.


An gabatar da Malamin Sheikh Abduljabbar Kabara a gaban kotun a ranar 16 ga watan July, 2021 bisa zargin kalaman ɓatanci da rubuta al'umma wanda suka saɓa da sashe ba 392 (b) na ACJL, zargin da Malamin ya sha musantawa. 


Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola ya yanke hukuncin a yau Alhamis 15 ga watan Disamba, 2022 ya kuma yi umarnin a kwace masallatai biyu da malamin yake da su, Masallacin Ashabul Kahfi dake Gwale sani mai Nagge, da kuma Jami'urrasuli dake tukuntawa gidan maza a jihar Kano. 


Kotun ta kuma yi umarnin haramta wallafawa ko sanya hotunan sa da sunan yada manufar sa, ta kuma haramta tallata aƙidar sa da sanya karatukan sa a gidajen Radio, talabijin da kuma kafafen sada zumunta,  ta kuma yi umarnin ga gwamnatin jihar Kano da ta da yan sanda su kama duk wanda ya saba wannan umarnin. 


Farfesa Mamman Lawan Yusufari SAN wanda yayi magana a madadin lawyoyi masu gabatar da ƙara ya sheda cewa sun gamsu da wannan hukuncin da Kotun ta yankewa Sheikh Abduljabbar. 


Saidai a nashi bangaren, Sheikh Abduljabbar Kabara ya hakurkurtar da mabiyansa inda yace zai yi mutuwa ta girma, kuma baya rokon sassauci daga mai Shari'a. 


''Ni bana neman sassauci akan wannan laifi da ban yi ba, ina bawa masoyana hakuri, kar su samu damuwa kan tafiya ta lahira, zanyi mutuwa ta girma, kuma bana neman kai Ibrahim Sarki kayi mun sassauci, kuma a gaggauta yi mun hukuncin nan. Kalami na na karshe kenan. '' inji Sheikh Abduljabbar. 


Saidai bamu samu jin ta bakin Barista Aminu Ado wanda ya rikewa Barista Dalhatu Shehu Usman a matsayin lawyan wanda ake ƙara sakamakon ficewar sa da wuri bayan kammala shari'ar, kuma bamu same shi a waya ba har zuwa kammala wannan rahoto.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post