@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
1. Bayan mintina 20: Hauhawar jini da saurin bubbugawar zuciya za su ragu.
2. Bayan awanni 12: Gurɓatacciyar iskar nan mai guba (carbon monoxide) za ta daidaita a cikin jini.
3. Bayan sati 2 – 12: Zagayawar jini da aikin huhu za su haɓaka.
4. Bayan wata 1 – 9: Tari da gajercewar numfashi za su ragu.
5. Bayan shekara 1: Haɗarin samun cutar jijiyoyin jini da ke bai wa zuciya jini zai ragu da rabi.
6. Bayan shekara 5: Bayan shekara 5 – 15 da ƙaurace wa shan taba sigari, haɗarin kamuwa da shanyewar ɓarin jiki zai yi daidai da na wanda bai taɓa sha ba.
7. Bayan shekara 10: Afkuwar mutuwa daga cutar daji / kansar huhu za ta ragu zuwa rabi. Haka nan, haɗarin kamuwa da cutar dajin / kansar baki, maƙogaro, mafitsara, ƙoda da matsarmama za su ragu.
Ƙaurace wa shan taba a yau!