Hankali da Ilimin!!!

 


@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@


(1) Manzon Allah sallallahu alaihi wa aleh an ruwaito cewa ya fadawa guda daga cikin sahabban sa cewa a cikin ko wanne abun halita akwai wani Abu da yake sarrafa shi har ya zama Abinda yake iya zama! GA dabbobi shine Qarfin zuciya,  (courage) GA masu imani kuma shine hankali, Ina bincike domin Nemo wannan hadisin,  


( 2) An ruwaito cewa Imam Ali alaihi Salam yana cewa in kana son haskaka zuciyar Ka da imani to Ka sanya ilmi ya zama shine kamar kyandir Hankali kuma ya zama harshen wuta! 


(3) Nana  Aisha Allah ya qara Mata yarda tace cikin sahih Muslim in kana karanta alqur'ani baka samu nutsuwar hankali ba to kabar shi,  tana bada labarin lokacin da tazo ta samu Manzon Allah sallallahu alaihi wa aleh yana karanta aya ta bakwai cikin surah Ali imran,  


(4) An ka6o daga Abu ja'afar Muhammad baqeer alaihi Salam yace bayan Allah subhanahu wata'ala ya qare halitta sai ya umarci Hankali da cewa ya matso gaba gare shi, sai Yayi,  sai zati yace ya koma muqamar sa, shima ya koma sai madaukaki yace ina rantsuwa da zati na da kuma buwaya ta ban halicci wani Abu mafi soyuwa a waje na sama da kai ba! 


(5) Imam Musa ibn ja'afar, Alaihi Salam yace yakai Hisham ba'a sanin Allah ko a bauta masa sai kana da hankali! 


Hatta yan wuta sukan yi kuka ne da cewa da sun Kasance sunyi amfani da hankalin su da basu shiga cikin wutar ba!  Kamar

 yadda  yazo cikin suratul mulk aya ta 10 


Na zurfafa bincike na na fahimci cewa malamai suna gaba da kasancewar yin amfani da Hankali a saman ilmi ne domin wasu dalilai kamar haka! 


1) Idan zaka yi amfani da ilmi to zaka haqura da ganin Girman kowa bayan Allah da Manzon sa sai manyan bayin allahn da suka tsarkaka daga barin qarya! !  Su kuma malamai suna ganin girman wasu Don haka Baza su Baka irin wannan ikon tunanin ba! Suna cewa magabata ba ma'asumai bane Amma baka isa Kace GA lefin su ba! 


2) in zaka yi aiki da hankali cikin sauqi zaka gane qarairayin da wasu suka yi wa musulunci wanda a qarshe zai zubar da Girman wasu wai su magabata, wanda yin hakan bazai yi wa su kuma malaman nan dadi ba shi yasa suka zare Maka hankali cikin sauqi suka qarfafe Ka da ilmi Amma in kazo sanin Allah wanda yake wajibi ne Akan Ka sai kayi ta kokonto in kana ibada! 


3) da yake addinin musulunci origin din sa daga larabawa yake su kuma mutane ne da suka dauki kan su tun a wancan zamanin cewa su a lungu suke sune Qarshen Waseca a duniya shi yasa har yanzu basu dena fada da civilization ba!  Wannan al'adar tabi jikin musulni har cikin qasar hausa, Amma musulmin da suke ba larabawa ba

: Irin musulmi farisawa, ko turkawa,  ko kurdawa da maley duk sun barwa larabawa al'adar su ta yin fada da hankali, a yau in kana neman ci gaba a qasashen musulni a wajen su kawai zaka samu ba zaka samu qasar larabawa ko guda daya ba a Fannin ci gaban zamani saboda yawan Mai da kawunan su baya da suke kamar Malam bahaushe,,  


Idan na samu qalubale Qwarai zan fadada!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post