@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
Hukumar da ke sa ido kan gandun daji a kasar Habasha, ta ce ta sha damarar yaki da kurayen da ke addabar mutane a wajen birnin Addis Ababa.
Cikin shekara biyu kurayen sun yi ajalin mutane akalla 8, saboda munanan hare-haren da sukei wa mazauna garuruwa da kauyan kasar.
Shugaban hukumar da ke sa ido kan gandun daji a Habasha, Banki Budamo, ya shaidawa BBC cewa hare-haren su na shafar mata da kananan yara har da tsofaffi.
Sai wai wasu kwararru na cewa kara fadada gidaje da share bakin daji da mutane ke yi domin gina gidaje ya kara tunzuro dabbobin masu hadari zuwa inda mutane suke.
A farkon watan Disamba, wata kura ta far wa wani mutum tare da hallaka shi a cikin sabon gidan alfarmar da ya gina na zamani a garin Lege Tafo mai nisan kilomita 17 daga Addis Baba.
Har wa yau, mazauna garuruwan da ke kusa sun sha bada rahoton jin kukan jama'a da daddare na neman dauki, idan kurayen sun kai mu su hari, amma babu yadda za su iya fita domin taimakawa.