@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
Daga Mukhtar Halliru Tambuwal, Sakkwato
Gidauniyar Qatar Charity Foundation dake da ofishi a Nijeriya, ta gudanar da ayyukan sama da naira bilyan biyar na tallafi tare da ayyukan jin ƙai daban-daban a Jihar Sakkwato.
Shugaban Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato, Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato) shi ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin tallafin karatu na Gudauniyar Qatar wanda aka gudanar a harabar hukumar a ranar Litinin 19 ga watan Disamba, 2022 daidai da 24 ga Jimada Ula 1444 BH.
Malam Muhammad Lawal Maidoki ya ƙara da bayyana cewa waɗannan ayyuka da Qatar Charity ta samar ta hanyar hukumarsa sun taimaka sosai wajen inganta rayuwar al'ummar jihar.
A cewarsa, cikin abubuwan da Gudauniyar ta gabatar sun haɗa da gina masallatai fiye da 100, da rijiyoyin burtsatse, injinan niƙa da ɗinki guda 300 da kuma rukunin gidaje 150 da aka gina wa ‘yan gudun hijirar Gundumar Gandi a Ƙaramar Hukumar Raɓah.
An kuma samar da kayayyakin aikin kafinta da na famfo, guda 9 na Keke Napep ( Tricycles) da kuma sandunan makafi da kuma ɗaruruwan kujerun guragu ga masu fama da nakasa a faɗin gundumomi 87 na jihar.
A halin yanzu Qatar Charity ta sake ɗaukar marayu mabuƙata 1200, don samun tallafin karatu wanda zai kai matakin karatunsu na jami'a daga cikin su an fara tantance 250 don cin gajiyar shirin Qatar Back To School Program wanda aka fara don tallafawa marayu marasa galihu da kayan ilimi.
Ya kara da cewa kayan tallafin sun haɗa da kayan makaranta da kayan rubutu da jakunkuna da kuma littattafan rubutu domin sauƙaƙa musu harkokin ilimi.
Shugaban ya ƙara da cewa, haɗin gwiwar tsakanin Qatar Charity da hukumar sa, ya yi tasiri ta fuskoki da dama tare da ba da tabbacin samun ƙarin cigaba ga al’ummar Jihar Sakkwato musamman marayu da kuma waɗanda basu da gata a cikin al’umma.
Don haka Malam Muhammad Lawal Maidoki ya yi kira ga ƙungiyoyin kamfanoni da su yi koyi da Gudauniyar Qatar Charity don amfanin talaka.
A nasa jawabin Daraktan ƙungiyar agaji ta Qatar Sheikh Hamdi wanda ya yi magana ta bakin shugaban sashin tallafawa marayu da jama’a Shu’aibu Atiku Gombe, ya ce shirin Komawa Makaranta an yi shi ne domin a taimaka wa marayun da kayan karatu, da nufin ƙarfafa musu gwiwa kan cigaba da neman ilimi.
A cewarsa, gidauniyar tana bayar da tallafi ga marayu, iyalai, ɗalibai da nakasassu a duk faɗin duniya ta hanyar Waƙafi da aka samu daga al'ummar kasar Qatar.
Sheikh Hamdi ya kuma bayyana gamsuwa da godiya ga hukumar zakka bisa jajircewar da take yi wajen ganin an kyautata rayuwar marayu tare da samun nasarar ayyukan agaji na Qatar Charity a Jihar Sakkwato da ma wajenta.
Tun da farko Babban Bako na Musamman Gwamnan Jihar Sakkwato, RT. Honarabul Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana irin gudunmawar da Gidauniyar Qatar Charity ta bayar a matsayin mai matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa ilimi da zamantakewar al'ummar jihar, tare da yin alƙawarin ƙarin haɗin gwiwa da Hukumar Zakka da Waƙafi ta jiha da gidauniyar.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato, Alhaji Muhammad Mainasara Ahmad (mni) ya yabawa shugaban Hukumar Zakka da Waƙafi bisa nasarorin da ta samu a wasu tsare-tsare da haɗin gwiwa tare da yin alƙawarin cigaba da tallafawa hukumar domin isar da wasu abubuwa masu muhimmanci ga al'ummar jihar.
Da yake jawabi Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana shirin a matsayin wanda ya dace da lokacin da za a bi wajen samar wa marayun ilimi mai inganci cikin sauƙi wanda zai sa su zama masu riƙon amana da al’ummarsu. Sarkin wanda ya samu wakilcin Ubandoman Sakkwato Sabon Birni Sheikh Malami Muhammad Macciɗo,
ya shawarci waɗanda suka amfana da su yi kyakkyawan amfani da tallafin domin cimma burin da aka sa a gaba.
An dai kammala bikin ne da wasan kwaikwayo kan muhimmancin ilimi da wasu marayu da suka gabatar wanda ya faranta wa waɗanda suka halarta rai.
Taron ya samu halartar Shugaban Ma'aikata na Jiha, uwayen ƙasa, wakilin UNICEF, malaman addini, uwayen mayaru da manema labarai.