Gaskiya Ɗaya ce !!!

 

Copy




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]



Shin kayi nazari cewa a yau a wannan zamanin naka babu me jarumtaka irin ta wannan waliyi ?


(1) Duk wani rashin mutunci da  ta'addancin da Ibn taimiyya ya koya wa mabiyyan sa na gida ( izalawa ) da kuma 'yan izalar daji ( Boko Haram), wannan gwarzo shi kaɗai ya hana su sakat, ta hanyar yaye duhun da Ibn taimiyya ya jefa su ciki, wannan tasa a kullum suke asarar mabiyan su, masu neman gaskiya.

Koni ta sanadiyyar yaɗa karatun sa da nake 'yan izala da yawa sun bar izala, kuma har gobe suna mutunta ni.( Alhamdullah).


(2) Da Ni ɗan faira ne, a raina ina ganin babu Wanda ya kaimu dace a wajen Allah, kuma a kaf waliyan ALLAH babu kamar Inyass kuma Ɗarikar Tijjaniyya ita ce cikakkiyar hanyar gaskiya. Amma haɗuwa ta Sheikh Abduljabbar tasa wallahi na fahimci cewa shi Allah bada ƙungiyanci yake amfani ba da zuciya yake, kuma babu wanda yafi Wani ko a cikin Sahabbai illar wanda yafi wani tsoron Allah.

Da matsalar Haƙiƙa ta taso na fahimci cas'in da tara daga Malam Tijjaniyya maƙiya gaskiya ne, basa son gaskiyar da Sheikh Abduljabbar ya ke gaya musu,, hakan tasa na bar Tijjaniyya. Kuma har gobe ina gode Allah akan haka.


(3) Ƙadiriyya(  ƙadiriyya salafiya, junudun min junudul asad,) wannan shine taken da muke musu, wato me unguwa da jama'ar sa. Su kuma wannan na ukun Sun fifita duniyar su akan lahirar su. Sun haɗa kai da duk wani maƙiyi dan suga sun disashe hasken da Allah ya azurta gidan su da shi.Wannan tasa M, Abduljabbar yaja gefe, yayi aiki tuƙuru, birni da ƙauye, ƙasa da ƙasa, kuma Allah ya albarkaci aikin, yau kuma sai ya zama so suke suga bayan sa,ko ta ƙaƙa.


(4) Jama'ar gari:

Allah ya yi mu cikin al'ummar da bata amfani da hankali wajen 'yin hukunci.

Duk sharrin da aka maka kawai sai jama'ar gari su yarda. Saboda kidahuman ci. Misali.

A yau na ƙai shekara sha takwas in bin Malam Abduljabbar,  kuma duk karatun juma'a da na Lahadi baya wuce ni. Amma kuma wai ni wani zai gayan malam ya taɓa Annabi. To wallahi dukkan ku yafi ku ƙaunar Annabi ( S.A.W).

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Wannan bata hakka yake kuma allah yafisu

    ReplyDelete
Previous Post Next Post