GARIN DAYAFI YAWAN SHAHIDAI A WAKI'AR 12/12/2015!!!

 




Dakace sunan wani gari ne a Cikin lardin zazzau, yananan Sama kadan da birnin zariya a gabashi akan hanyar jos shine gari na farko da zaka soma taraswa tsakaninsa da Darur Rahama gari daya ne wato dambo in zakaje yana hannun hagu in zaka dawo yana hannun dama,Gari ne mai tsohon tarihin harkar musulunci a cikinsa akwai 'yanuwa musulmi Almajiran sheikh Ibrahim zakzaky(H) Tun tele tele kun sunsha fuskantar waqi'o'i daban daban Tun kafin waqi'ar abacha,'yan tauri da da 'yan sahihul Jihad sun buga sun barsu da waqi'ar abacha tazo an samu shahidai da wadanda aka kama aka tsare bisa zalunci,amma dai haka suka daure tare jajircewa wajen ci gaba da yada da'awar musulunci har aka sami tsayayyar da'ira ta 'yan uwa, wahabiyawa da sauran maqiya basu daina aikinsu na suka da Karya da sharri ga 'yanuwa na garin amma irin jajircewa da kyakkyawar mu'amala da sauran al'umma da 'yanuwan garin keda shi, shi yake kunyatar da maqiya har Allah ya kawo mu wannan lokaci 




wannan waqi'a ta mauludi data gabata ta Kara fito da jarumtar 'yanuwa na garin Dakace domin daya bayan daya idan kayi wa nijeriya anguwa anguwa to da wuya a sami inda yafi Dakace yawan shahidai ko kuma wadanda ba labarin su domin I zuwa yanzu ana lissafin 'yan uwa 17 ne basu ba labarin su,wasu an tabbatar da sojojin nijeriya 'yan inada kisa sun kashe su wasu kuma ba labarin su, kuma dukkansu a gyallesu, kasantuwar Dakace itace unguwa mafi kusa da gyallesu, sannan akasarin 'yan uwan garin Harisawa ne kuma duk ranar asabar itace ranar duty Na harisawan garin kuma waqi'a ta auku ranar asabar ne bugu da Kari jarumai ne, ko ma a'ina waqi'ar ta auku kuma kowacce rana ce ma zasu kai kansu, baya ga shahidai akwai wadanda aka jikkata da dama akwai kuma wadanda suke Kaduna a tsare, inkaje Dakace yanzu zaka taras da matan shahidai da 'ya'yansu da dama abin gwanin ban tausayi, kuma babu wani gida da ba a sami Shahidi ba, amma akwai abinda zai karfafa maka gwiwa shine yadda da'irar ta koma daram kamar wani abu bai faru ba, kuma a Cikin wadanda aka kashe harda Amirin garin Malam Abbas da sauran masu bada gudunmawa, Amman duk da haka komi na harkar musulunci yaci gaba,wannan shine abinda kowa ke mamaki a garin a zaton maqiya komi ya Kare kenan, kawai sai suka ga Allah ya tashi wasu ma'aikatan, kai Dakace lallai garin shahidai ne!!!


Daga dan uwanku Muhammad Rajab



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post