[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Malama Salaha Hari Jamo baiwar Allah ce mai matuƙar haƙuri, sannan kuma an shede ta da son addini da yawan ibada, ga shi Allah Ta'ala ya yi mata baiwar yawan sadaka da kyauta, kuma takan yawaita cewa ƴaƴanta da duk wani mai mu'amala da ita, ya zama mai haƙuri da riƙo da addu'a.
Akwai wasu lokuta idan su Sayyid Zakzaky Hafizahullah suka tafi Hussainiyya Baƙiyyatullah, sai ya zama gidan ba kowa sai Mama, to wata rana sai Mama ta ga Sayyida Zahara (s.a) ta zo mata, suka daɗe suna fira, da su Sayyid Hafizahullah suka dawo, sai tace masa; yau Ƴar Manzon Allah (SAWW) ta zo wuri na, mun yi ta fira, sai ta cewa Sayyid (H); Ashe ba ta da jiki, ita ba doguwa ba, kuma ita ba gajeruwa ba.
-Aba Sajjadi ne ya rubuto muku daga cikin Littafin Tarihin Malama Salaha Hari Jamo.
Allah Ta'ala ya ƙara Lulluɓeta da Rahamarsa.
Allah ya sanya ta a ceton Sayyada SA.
ReplyDeleteAllah ya jaddada rahama agareta.
ReplyDeleteKuma dama aibabu wani abin ban mamaki domin kuwa mijinta' jikane sayyidah (as).
Gashi ta haifi.
Shima ya haifi waliyyai.
Sukuma sunata samar takiyyai.
MALAMA SALAHA TA DABAN CE ACIKIN MATAN WANNAN QARNIN.