[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Sheikh Qasiyuni Ya Fasa Ƙwai inda ya rubuta a shafinsa cewa....
Ranar addu’ar uku Talata 08/10/1996 , Shaikh Yusuf Makwarari R.A ya jagoranci daukacin Qadirawa sukayi caffa ga daukacin ‘ya ‘yan Malam a matsayin Halifofin sa, Ni kuma Al-Qasiyuni na ari bakin ‘yan uwana bada shawartar su ba na nada Alh. Qaribu a matsayin Halifar Malam.
Malam bai nada wani a matsayin Halifar sa ba; Allah ne shaida banyi haka ba sai dan asirin gidan ya rufu kan Qadirawa ya hadu, sai dai kaddara ta riga fata, wanda nayiwa bajintar bai godewa Allah ba , ya raba kawunan mu, ya tozarta gidan, har takai yau shine jagoran makiya a gidan wajen yiwa kanin mu kazafin zagin Shugaba (Waliyazubillah), Ni kuma yau shekara biyar yayi amfani da ‘yan daba da police ya hana ni gabatar da karatuka da tarukan Addini da nake gabatarwa a gidan , Karatun Asshifa kadai ya rage shima yayi iya yin sa Allah ne bai nufa ba.
Wannan bayani nayi shi ne don wanzar da gaskiya, ba don muzantawa ko kai kara ga wani mahluki ba.
Da Allah na dogara
kuma gare shi nake kai kukana.