@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
Fadak na daga cikin mas'alolin Tarihi da aka kai ruwa rana kanta tsawon ƙarni 14 a tarihin Musulunci , Musamman tsakanin marubuta da ra'ayoyinsu suka banbanta game da sha'aninta , kama daga masu fito da muhimmancinta a Tarihi da kuma waɗanda suka ƙasƙantar da sha'aninta da ganin cewa bai kyautu a bata wani muhimmanci ba , musamman da Ayoyin Kur'ani da ruwayoyin Tarihi suka tabbatar musu da ƙwace wannan wuri da aka yi , har ta kai ga Wani Mutum na cewa a fadawa ƴan Shi'a su faɗi farashin wurin zai biya Nana Faɗima (a.s) ! Irinsu Ibnu Taimiyya L kuma suka Danganta Nana Faɗima (a.s) da miyagun Kalmomi saboda ta nemi haƙƙoƙinta ciki har da wannan Fadak ɗin , duk da ba Abun mamaki bane magabatansa ma sun kamanta Sayyida Faɗima da Ummu Ɗuhaal ne kai tsaye !
MECECE FADAK A TARIHI ?
A zahiri Fadak wata Alƙarya ce dake cike da Gonaki da Lambuka masu tarin yawa da alkhairai da Galibi ake Noma Alkama da Dabinai tun bayan an buɗe garin Khaibar sai Manzon Allah (saww) ya aikawa Yahudawan FADAK da saƙon su amsa kiran Addinin Musulunci, amma sai suka yi Sulhu dashi akan su bashi Fadak , sai ko Annabi (saww) ya amsa musu tare da yarjejeniya .
Daga nan kuma sai ya bawa Sayyida Faɗima (a.s) wannan wuri tunda haƙƙi ne nashi (a Keɓance) domin ba da yaƙi aka buɗe wurin ba , musamman da Ayar
وآت ذا القربى حقه .....
Ta sauka sai ya damƙata ga Sayyida Zahra (a.s) .
Ruwayoyi na Ɓangarorin duk Musulmi sun tabbatar da haka da hanyoyi tabbattattu mabanbanta , kuma faɗin Allah Ta'ala:
وَمَا أَفَاء اللَّهُ عَلَى رَسُولِهِ مِنْهُمْ فَمَا أَوْجَفْتُمْ عَلَيهِ مِنْ خَيلٍ وَلَا رِكابٍ....
Yana daga hakan .
Daga nan ne aka cigaba bayar da abinda ake samu daga wannan wuri ga Talakawan Banu Hashim da wasunsu .
To a bayan Shahadar Manzon Allah (saww) da aka yi dambarwar kafa Gwamantin Inqilabi sai aka ƙwace Fadak daga Sayyida Zahra (a.s) da danginta , ita kuma ƙari akan bijrewa wannan Gwanantin da ba ta Shari'a ba , sai tace : Lallai a dawo mata da haƙkoƙinta da Khumusin Khaibar da ita kanta Fadak ɗin , take aka ce mata ai Mahaifinta yace : Ba'a gadon Annabawa , kamar Yadda yazo a riwayar Bukhari da Muslim da wasunsu .
Ita kuma tace : Hakan sam bazai yu ba (don da hakan gaskiyane da ita za ta fi kowa sani a matsayinta Na mai gadonsa ) , kuma su kansu sun san bazata yi musu ƙarya ba domin sun shaida bayan Mahaifinta duk Duniya ba wanda ya kaita gaskiyar zance , kamar dai yanda yazo a Hadisin A'isha Bintu Abu Bakr .
Duk da hakan Sayyida Faɗima (a.s.) bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen kawo Hujjojinta na daga Ayoyi da Zantukan Mahaifinta da suke tabbatar da gaskiyarta , amma aka ce ba za'a karɓi zancenta da Hujjojinta ba , har ta kai ga anƙi Karɓar Shedunta da ta kawo aka ma Siffanta da "Ummu Ɗuhaal"Astagfirullah...... Daga ƙarshe da suka ga ta ƙuresu da Huɗubobin da ta dinga yi a Masallacin Manzon Allah (saww) , har mutane sun fara tasirantuwa da maganarta suna dawowa hayyacinsu da kukan takaici da nadama , sai fa aka kai mummunan hari gidan Nana Faɗima (a.s) da Mijinta da hujjar sunyi tawaye ga sabuwar Gwamnati mai ci har hakan yayi sanadiyar Shahadarta ...Allahu Akbar .
Duk da dai Annabin Wahabiyawa Ibnu Taimiyya a cikin Minhaj ya ce : Wannan hari an kaishi ne domin a bincika ko akwai haƙƙoƙin Allah da aka ɓoye a gidan domin a kwaso a rabawa masu shi , inda yake cewa :
وَغَايَةُ مَا يُقَالُ: إِنَّهُ كَبَسَ الْبَيْتَ لِيَنْظُرَ هَلْ فِيهِ شَيْءٌ مِنْ مَالِ اللَّهِ الَّذِي يُقَسِّمُهُ، وَأَنْ يُعْطِيَهُ لِمُسْتَحِقِّهِ، ثُمَّ رَأَى أَنَّهُ لَوْ تَرَكَهُ لَهُمْ لَجَازَ ; فَإِنَّهُ يَجُوزُ أَنْ يُعْطِيَهُمْ مِنْ مَالِ الْفَيْءِ.
Duba Minhajul Bid'atil Umawiyya nashi Juzu'i na 8 , Shafi na 291 kaga wannan Maganar .
Shi ko Muhammad Bn Salihul Uthaimin cewa yayi :
Saboda tsananin Jayayya da Musu Sayyida Faɗima ta rasa hankalinta har bata ma san me take faɗa da aikatawa ba , in ba haka ba taya za ta ja da Khalifan Mahaifinta? Har ma yace wai Allah ya yafe mata wannan abu da ta aikata na ƙauarace masa da tayi .Mhm ! kaji Shafaffu da mai , Duba Ta'aliqin da yayiwa Shahihu Muslim a Juzu'i 9 Shafi 78 za kaga yana cewa :
اللَّهُمَّ اعفُ عنها، وإلَّا فإن أبا بكر رضي الله عنه ما استند إلى رأي، وإنَّما استند إلى نصٍّ، وكان عليها أن تقبل قول النبي عليه الصَّلاة والسَّلام: "لا نُورَث، مَا تَرَكْنَا صَدَقَةٌ"، ولكن عند المخاصمة لا يبقى للإنسان عقل يُدْرِك به ما يقول أو ما يفعل أو ما يتصرَّف فيه، فنسأل الله أن يعفو عنها عن هِجْرتها خليفةَ رسول الله صلَّى الله عليه وعلى آله وسلَّم).
Maganganun ire-irensu suna nan jingim da suke sukar Sayyida Fatima (a.s) dan ta nemi haƙƙinta a wajen Sarki na Farko , da munso za mu ware Silsilar Rubutun da zai fito dasu .
AƘIDA
Sai dai ita Fadak ba wai iya Alƙarya da gonaki bace kawai , a'a ! Fadak tana daidai da Imamanci da Khalifanci ne , domin kuwa yarda da cewa Fadak haƙki ne na Sayyida Fatimatuz Zahra (a.s) na lazimta yarda da Imamanci da Kahlaifancin Mijinta a bayan Annabi (saww) .
Wannan ɗaya ne daga cikin dalilan da suka sa aka ƙi yarda da bata dukkan haƙƙoƙinta ,