@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
"Dukkanin wanda duniya ta aure shi bazai taɓa ganin gudun ta ba, kullum zata ke ruɗarsa ne tana nuna masa cewa akwai sauran rayuwa mai tarin yawa a gaba gareshi. Baya nuna masa rashin tabbacin sa a cikinta balle yayi ƙoƙarin komawa zuwa ga mahaliccinsa Allah"
-
"Babu mai ƙaramin tunani kuma mara sanin ya kamata kamar irin wanda zai riƙi duniyarsa ita ce ƙololuwar burinsa. ya fi ba ta muhimmanci fiye da lahirarsa, yana fifita duniyarsa a kan lahirarsa, ba ya hangen gudun ta kullum dauwamarsa yake hangowa a cikinta ba ya hango ƙarewarta"
-
"Kullum ka kasance mai yawan yin tanadi a rayuwarka game da sha'anin mutuwa, rayuwar ƴar kaɗan ce, kullum mutuwa ake ta yi, kada ka shagaltu da duniya da abinda ke cikinta, ita duniya ba gidan zama bace, duniya aro aka bamu, kuma komai nata mai ƙarewa ne, kana cikin tsaka da rayuwarka mai cike da jin daɗi a cikinta sai kaji har lokacin ka ya shuɗe ba tare da ka ankara ba. Duniyar gudu take yi rayuwar kullum ƙarewa take yi. To ka alkinta lahirarka tun gabanin duniyarka ta ƙare".
Allah Yasa Mudace....
Tags:
Tunatarwa