... Umar Hassan Gololo...
Kafin a zageka, a maka sharri da kazafi, a yi maka karya, a Kama ka a tsare lallai an yiwa Malam Zakzaky(H).
Mun san wani lokacin da wadansu 'Ya'yan baya ga dangi suke cewa wai Malam Zakzaky(H) yana tura 'ya'yan mutane ana kashewa amma nasa suna gida, amma abin mamaki da takaici da Gwamnatin ala-tsine ta Goodluck Jonathan da Gwamnatin tir da Allah-Wadai ta Buhari suka kashe 'Ya'yansa shida murna wadancan kidahuman suka yi.
Ba a cikin Harkah Islamiyyah ba, hatta a cikin mutanen gari akwai wani mutum wanda aka yi masa dabbanci, wauta, mugunta da zalunci irin wanda aka yiwa Malam Zakzaky(H) a Nigeria?
Tun daga kan Obasanjo a khaki ake kama Malam Zakzaky(H) har zuwa kan General Buhari a farar hula, amma babu daya daga cikinsu da ya taba samunsa da laifin komai.
Duk abinda azzaluman Shugabanni da Miyagun Malamai da kidahuman talakawa suke yiwa Malam Zakzaky(H) yana kara masa yakini ne akan abinda yake yi na gwagwarmayar tabbatar addinin Musulunci, wanda yayi daidai da irin wanda ya faru da Annabawa da Manzanni Alaihimussalam.
Muna rokon Allahu Ta'ala ya karawa malam Zakzaky(H) kariya, juriya da lafiya, ya cika masa burinsa na tabbatar addinin Musulunci a wannan kasa dama Afirka baki daya, mu kuma Ya tabbatar damu a gwagwarmayar Musulunci karkashin jagorancinsa Alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi wa sallam.