DUK KAFIRAN DUNIYA SUNSAN CEWA, SHI'A MUSULUNCI SUKEYI. Cewar Sheikh Yaƙub Yahaya Katsina.

 


___Daga Hassan Abubakar Ahmad Ɗan Sister Katsina.


Akwai abun, banmamaki ace Natan yaawo ya gane  cewa, "Shi'a Musulunci suke' Ubama, shima yasan cewa, Shi'a Musulunci sukeyi, kuma dukkanin kafiran Duniya sunsan cewa, Shi'a wato ai nafin Musulmi ne. Kuma sune ƙarshen tsarinsu na kafirci. Amma abun, banmamaki waɗanda muke Sallah tare dasu a Masallanci ɗaya, muna cin Kasuwa ɗaya, Unguwa ɗaya, Gari ɗaya, Harshe ɗaya, kuma dangin Juna amma ace Mutum shi ya kasa ganewa.


Saboda haka sai yana ganin wani abu daban wannan abun, da kake gani Musulunci ne, kuma sun kansun kafiran Duniya har Ubama yace abunda akayi wa Shi'a ba dai-dai bane. To yaushe wani Musulmi mai sheda "La'ila'wa'illalla-Muhammad'Rasullilah" muna cin Kasuwa ɗaya dashi, Masallanci ɗaya mu haɗu gurin Suna: da ɗaurin Aure shikuma har yanzu kwakwalwarsa bata gane masa ba. Shi wani abu yake gani daban.


Akwai abun, banmamaki, Sunan da ka kira kanka dashi Adalci a kirashi dashi. An riga an samun ansa Iyayenmu, ansan inda muka taso, ansan taya muka faro Addininmu, ansan Malaman da mukayi Karatu wajensu, anajin Maganganun mu, anajin Litattafan da muke karantawa, anajin Ayoyin da muke karantawa. Amma har yanzu wasu sun bushe Idanunsu kawai ba Addini ake ba. Saboda Minene?


Wannan ɗan tsakanin abubuwa sun daɗemana da bayyanar mana ƙarara cewa! "wata Kwangilar ce, gagaruma aka karɓo kuma munyi mamakin wnnan Kwangila. Wallahi Kwangila ce, aka amso gagaruma, cewa, sai anga bayan wannan kiran". Saboda  wannan kiran shi ne zai kawo sauyi a ƙasa. Shi ne zai dawo da turbar Shehu Usman Ɗan Fodiyo (R.a) da tawuce muna baige muna shauƙi. Shi ne zai kawo ƙarshen wannan Zalincin da muka shekaru muna da kon shi, bai biya mana buƙata ba. 


H. Ɗan Sister Katsina.

11/December/2022 M.



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post