Imam Mustafa Adinga , Ɗaya ne daga cikin Manyan Malamai a Ɗariƙar Tijjaniyya da suka yi fice wajen faɗa da Malam Abduljabbar tun sama da shekara 10 baya , Almajirin Farfesa Maƙari ne kuma Limami ne a Abuja , Amma ya fito ya yi ƙoƙarin fadar gaskiya da adalcin da dayawan Malamai suka kasa fitowa suyi saboda son zuciya ko wata maslaharsu.
Wallahi Tallahi bamu ce Malam Abduljabbar baya kuskure ba , kuma bamuce duk wata fahimta tashi haka take ɗari bisa ɗari ba ko dai-dai ce , sai dai !
Duk mai hankali da tunanin yin Adalci yasan akwai lauje cikin naɗi game da sha'anin Malam Abduljabbar Kabara (H) .
Tabbas Siyasar Addini , Siyasar Jam'iyya, Siyasar Family ne suka haɗu da Ƙarfin Gwamnati da jahilci da wautar wasu mutanen gari dan suga bayan Malam Abduljabbar (H) ta kowacce hanya , abune da ya fi rana bayyana ga duk mai idon basira da zuciyar ganin gaskiya........
ليت قومي يعلمون !
ليت قومي يفهمون !
Wallahi su kansu sun san ƙarya suke Sheikh Abduljabbar yafi su ƙaunar Annabi da bashi kariya , su kansu sun san ƙarya suke Malam bai taɓa janabin Annabi ba kuma baya nufin hakan . Allah dai yana nan a madakata .